Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Biliyan Guda A Jana’izar Alex Ekwueme –Ngige

Ministan kwadago da samar da ayyuka, Dakta Chris Ngige, a jiya ya bayyana cewa,gwamnatin Tarayya ta kashe Naira Bilyan guda ne a wajen jana’izar Ekwueme.

Hakan ya biyo bayan gyara dukkanin hanyoyin da suke isa kauyen tsohon mataimakin Shugaban kasan ne, da suke a Karamar Hukumar Orumba ta arewa, cikin Jihar Anambra, domin shirye-shiryen jana’izar.

Alex Ekwueme, ya mutu ne a wani asibiti da ke Ingila a shekarar da ta gabata, wanda kuma aka sanya ranar jana’izar na shi daidai da 19 ga watan Janairu 2018.

Ministan,wanda yake wakili ne, a kwamitin shirye-shiyen jana’izar, ya bayyana hakan ne a sa’ilin da ya kai ziyara Oko, domin ya duba yadda aikin ke tafiya. Ministan ya nu na gamsuwarsa da yadda aikin hanyan ke tafiya, ya kuma ce dan kwangilar ya tabbatar masa da cewa,za su kammala aikin kafin ranar da za a soma bikin jana’izar, watau ranar 1 ga watan Fabrairu 2018.

Kabarin wanda gwamnatin Tarayya ta gina, an kammala gina shi, a ranar Talatan nan ne dan kwangilar ya yi alkawarin hannanta mana shi. Ita ma gwamnatin Jihar Anambra tana nata kokarin, domin ta gina wasu hanyoyin a yankin domin jana’izan.

Ngige ya ce, “Baya ga mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, manyan jami’an gwamnatin Tarayya ne ake sa ran za su halarci jana’izar. Da yake karin haske kan rade-radin da wasu ke yi na cewa, Shugaba Buhari, bai yi abin a zo a gani ba, kan shirye-shiryen jana’izar, Ministan ya ce, abin da gwamnatin Tarayya ta kashe a kan jana’izar, bai gaza Naira bilyan guda ba.

Iyalan mamacin sun san dukkanin kokarin da gwamnatin ta Tarayya ke yi a kan jana’izar, “Dan mamacin na farko, Pastor Obi Ekwueme, yana cikin wakilan gwamnatin Tarayya na shirin jana’izar, sannan kuma an yarje masa da ya tura wakili guda a cikin dukkanin sauran kwamitocin da muke da su.

 

Exit mobile version