A tsakanin 2017 da 2018 gwamnatin Nijeriya ta kashe akalla naira fiye da biliyan 1.8 don ciyar da kananan yara wadanda suke famma da wahalar matsananciyar yunwa, a jihohi 18 dake cikn kasar.
Shugaban sashen yaki da kawar da yunwa na ma’aikatar kiwon lafiya Chris Isokpunwu ya sanar da hakan ranar Lahadi, lokacin da yake hira da Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Abuja.
Isokpunwu ya bayyana cewar sakamakon binciken da ma’aikatar kiwon lafiya ta gudanar a shekarar 2017 ya nuna cewa jihohi 18 a kasarnan na fama da matsananciyar yunwa.
Ya cigaba da bayanin cewar a dalilin haka ne ita gwamnatin ta tsaro matakai tare da hada hannu da Asusun kula da al’amuran gaggawa na kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) domin ganin ta kawo karshen wannan matsala a Nijeriya.
“Daga cikin Naira biliyan 1.8 da gwamnatin tarayyar ta samar da Naira miliyan 600 wanda ma’aikatar kiwon lafiya ta yi amfani da su wajen sayo magungunan, ta waje daya kuma ga kuma shi al’amarin horar da ma’aikata da kuma gina asibitoci.
Ya kara jaddada cewar a shekarar 2018 gwamnati ta kara samar da Naira biliyan 1.2 da hakan ya sa aka samu damar samun damar ciyar da yaran dake fama da matsananciyar yunwa a jihohi 12 na kasar.
Ya cigaba da bayanin cewar, “Da muka gano yawan jihohin dake fama da wannan matsalar a cikin kasar nan sai muka aika masu da wasiku domin sanar da su da matsalar dake tunkarar su da kuma irin taimakon da zamu iya yi masu. Sai dai kuma mun yi rashin sa’a domin kuwa da yawa daga cikin jihohi basu ce mana komai akai ba.”
Ya yi kira da jihohin da su amsa da kiran da ma’aikatar ta yi, bayannan kuma su mai da hankali wajen ganin sun kawar da matsananciyar yunwa wadda yara kanana suke fama da ita.