Maigari Abdulrahman" />

Gwamnatin Tarayya Ta Koka A Kan Musguna Wa ’Yan Nijeriya A Kasar Ghana

Ambasadan Nijeriya a kasar Gana, Michael Abikoye ya koka akan irin musgunawar da hukumar kula da shiga da fice ta kasar Gana ke yi ‘yan Nijeriya mazauna kasar, inda a tsakanin shekaarar 2018 zuwa 2019 aka maido da ‘yan Nijeriya kimamin 723 daga kasar zuwa gida Nijeriya.
Ambasada Abikoye ya bayyana hakan ne a yayin wani zaman ganawa da shugaban hukumar kula da shige da ficen kasar Gana, Kwame Takyi a kasar Gana.
Kwamishinan y ace, ‘yan Nijeriya mazauna Gana 723 ne aka maido Nijeriya bisa zargin laifin
anfara a intanet, zama a kasar ba bisa ka’ida ba da kuma karuwanci.
Mutun 81 daga cikin wadanda aka maida Nijeriya, ana zargin su ne da aikata laifin danfara ta intanet da zama ba bisa ka’ida ba a tsakanin watan Janairu, sai mutum 115 da aka maida Nijeriya a watan Febrairu bisa zargin laifin aikata karuwanci a kasar Gana, inji Ambasadan na Nijeriya.
Ambasadan ya ja hankalin shugaban hukumar ta Gana da cewa, Gwamnatin Nijeriya ba za ta lamunhci duk wata muzgunawa ko azabtarwa wa ‘yan kasarta ba.
Ambasadan ya ci gaba da cewa, duk da yake, su ma hukumomin Nijeriya ba za su zura ido kan karya doka ko aikata laifi daga wurin ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasar ta Gana ba, to amma kuma, ba za su lamunce wulakanta ‘yan Nijeriya daga hukumomin kasar Gana ba.
‘Dalilin da hukumar shiga da fice ta kasar Gana ta bayar kan maido da ‘yan Niojeriya gida shi ne saboda aikata danfara ta intanet da karuwanci, to amman, bai kamata ba ace, za su kori ‘ya Nijeriya daga kasar ta Gana bisa zargin zama ba bisa ka’ida ba a kasar,’ inji Amabasada Michael Abikoye.
Ya ci gaba da cewa, ‘Akwai ‘yan kasar Gana da yawa da ke zaune a Nijeriya, amman Hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya ba ta taba korarsu ba saboda laifin zama ba bisa ka’ida ba, ba dan komai ba sai dan wannan ‘yan’uwan takar da ke tsakanin kasashen biyu.’
Daga bisani, Ambasadan ya mikawa shugaban takardar koke da ke dauke da bayanin ‘yan Nijeriyan da aka kora daga kasar daga watan Janairu zuwa yau.
Ya nuna bacin ransa da damuwarsa kan irin muzgunawar da ake wa ‘yan Nijeriya da rashin adalci a kasar, ya kara da cewa, akwai rahotanni da bayanai kan muzgunawa, cutatawa da azabtarwa da jami’an shiga da ficen kasar Gana ke yi wa ‘yan Nijeriya a yayin da su ke tsare da su a wurin tsare mutane kafin mayar da su kasar su.
Bai tsaya nan ba, sai da Ambasadan ya nuna wasu hotunan raunuka da karaya da wasu suka samu a yayin da ake tsare da su sakaamkon azabtarwa. Ambasadan y ace, hakan ya sabawa tsarin dokokin kasa-da-kasa kan muzgunawa wanda ake tsare da shi.
Daga karshe ya yi kira ga shugaban hukumar, da ya gargadi kunnen ma’akatansa da su dinga saka tausayi da adalci a yayin da su ke hulda ba ma da ‘yan Nijeriya kaai ba, a’a har da sauran kasashe, tun da su ba ‘yan ta’adda ba ne.
Haka kuma, ya nuna rashin jin dadin sa da irin yanda ake ajiye ‘yan Nijeriya a wurin tsare mutane a kasar lokaci mai tsawo gabanin maido su Nijeriya duk da takardar mayar da su da gaggawa kan lokaci daga Hukumar.
Da yake maida magana, Shugaaban hukumar shiga da ficen Gana din, ya bayyana cewa, eh haka ne akwai alaka da dangantaka a tsaakanin kasahen biyu kamar yanda Ambasadan Nijeriya ya fada.
To sai dai, halayyar wasu ‘yan Nijeriya ca ke tursasa hukumonin Gana korar ‘yan Nijeriyar daga kasar ta Gana, inji Shuigaban hukumar kula da shige da ficen kasar ta Gana.
A cewar Mista Takyi, baya ga aikata laifukan danfara ta intanet da karuwanci, to wasu ‘yan Nijeriya sun zama doka da kan su, ta yanda su ke abin da su ka so, ta yanda su ke tare manyan hanyoyin a kasar Gana a inda su ke shaye-shaye, fada da sauran su.
Ire-ire wadannan halayyar ne ya jaza aka bada umurnin kama duk wanda baya da lasisin zama kasar domin maayr da shi kasar sa.
To kuma dai, shugaban hukumar, ya yi wa Ambasadan alkawrin yin bincike kan zargin azabtarwar da y ace ana yi wa ‘yan Nijeriya.
A matsayin shaida kan irin abin da ‘yan Nijeriya ke yi a kasar ta Gana, Shugaban hukumar ya nuna wa Ambasadan wani bidiyo da a ciki ake nuna wasu ‘yan Nijeriya da su ka tare hanya ga motocin jami’an tsaron kasar bayan kama wasu ‘yan Nijeriya a unguwar Kasoa.

Exit mobile version