Gwamnatin tarayya ta rattaba hannun yarjejeniyar zuba jari da kasashen Morocco da Singapore, domin kara bunkasa harkokin kkasuwancin kasashen ketare. Sakataren dun-dun-dun na ma’aikatan kasuwanci da zuba jari, Dakta Nasir Sani-Gwarzo ya bayyana haka lokacin taron majalisar kasuwanci da zuba jari karo na 12 wanda ya gudana a garin Abuja ranar Litinin. Taron mai taken ‘farfado da bangaren masana’antu da kasuwanci da zuba jari a Nijeriya bayan wucewar cutar Korona’.
Dakta Sani-Gwarzo ya bayyana cewa, “mun yi kokarin wajen hada kai da ma’aikatar shari’a wanda shugaban kasa ya rattaba hannu a kan dokar sake farfado da hanyoyin zuba jari.”
Ya bayyana cewa, ma’aikatar kasuwanci tana aiki tukuru waje bunkasa zuba jari a jihohi 25 ciki har da Babban Barnin Tarayya, wanda yah ade har da bunkasa bangaren tsarin nan na shekarar 2020 zuwa shekarar 2030 tare da hadin gwiwar Bankin Duniya. Ya kara da cewa, suna kokarin yin shirin a dukkan hukumomi da ke kasrkashin ma’akatar wajen bunwasa su bayan wucewar cutar Korona, domin tauimaka musu wajen magance matsalolin da suka fuskanta lokacin cutar Korona. Sakataren ya ci gaba da bayyana cewa, ma’aikatan kasuwanci za ta sake bibiyan tsarin gudanarwa na kamfanoni a Nijeriya ciki har da shiurin nan na juyin juya hali na kamfanoni da tsarin kasuwanci, yayin da za a samar da tsarin zuba jari wanda za a shawarta masu ruwa da tsaki.
“Dukkan wadannan yunkuri za a gudanar da su ne idan aka kammala tattaunawa ta yadda za a samu nasarar inganta lamaarin cikin sauki,” in ji shi.