Idris Aliyu Daudawa" />

Gwamnatin Tarayya Ta Kwace Dala Miliyan 1 Da Gidaje Daga Iyalan Marigayyi Badeh

Ranar litinin ce babbar kotun tarayya dake Abuja ta yanke hukunci da kuma bada umarni na da a gaggauta rufe kamfanin Iyalikam Nigeria Limited wanda mallakin tsohon Shugaban rundunr tsaron soja ta Nijeriya, marigayi Marshal Alex Badeh.
Da yake an kama shi kamfanin da laifuka goma da suka shafi fataucin kudade, kamar dai yadda mai shari’a Okon Abang ya bayar da umarni na a kwace jkudade da suka kai dala milyan daya ($1m) da kuma gidaje na kawa, a wurare daban-daban cikin Abuja, wadanda aka nasaba su da shi Kamfanin.
Shi wannan hukuncin ya biyo bayan bayan da shi Kamfanin ya canza shawara, ta amincewar da ya aikata laifuka goma da suka shafi fataucin kudade wanda kuma tun farko shi Bade ya musanta hakan.
Maganar yarjejeniya da amincewa suna daga cikin abubuwan da ita Hukumar hana yi ma tattalin arzikin kasa tu’annafi wato EFCC, suka cimmawa da shi wandayake kare shi.
Su kaddarorin da aka nasaba su da shi Badeh da kuma Kamfanin Iyalikam, wanda shi mai shari’a Abang ya bayar da umarni na karshe cewar a kwace su, su kasance mallakar gwamnatin tarayya, an bayyana su cikin tsarin yarjejeniya da amincewa wadda kuma aka amince tare da ita Hukumar EFCC, abin da kuma Kotun ta san da hakan saboda an yi shio al’amarin ne tsakanin da lauyan kamfanin ranar litinin.
Kaddarorin sun hada da:
Wani babban gida a namba na 6, layin Ogun kasa da layin Danube Maitama, Abuja
Wani babban kanti a fuloti mai namba ta1386, Oda Crescent Cadastral Zone A07, Wuse II, Abuja
Babban gida mai namba ta 19, Kumasi Crescent, Wuse II, Abuja
Babban gida dake a namba na 14, akan titin Adzope Crescent, daura da Kumasi Crescent, Wuse II, Abuja
Sai kuma wani babban gida da yake a namba 8A layin Embu, kusa da Sigma Apartment Wuse II, Abuja
Da akwai kuma kudade dala milyan daya $1,000,000.00 wadanda aka samu a wani gida mai namba 6 layin Ogun kasa da layin Danube Maitama, Abuja.
Idan aka yi la’akari da ita yarjejeniya da amincewar da aka yi, Kotu ta da umarni na tunda an samu hujjar ta aikata laifin, dole ne shi Kamfanin a rufe shi, duk kuma wasu kaddarori mayar da su, su koma mallakar gwamnatin tarayya.”
Kafin dai mutuwar Badeh ita Hukumar tana shari’a da shi tare da kamfanin Iyalikam Nigeria akan laifuka 14 da suka shafi fataucin kudade, sai kuma yadda aka fitar da kuadade da suka kai fiye da Naira biliyan 3.97 daga cikin asusun ajiyar rundunar sojoji ta sama .
Badeh shi da kamfanin sun bayyana cewar basu aikata laifi ba, akan zargin da ake yi masu, a cikin shekararar 2016, wannan al’amarin ne kuma ya sa, aka ci gaba da sauraren maganar harkallar, wanda kuma daga baya aka rufe al’amarin sauraren ita karar shekarar data gabata, bayan da aka gabatar da shedu 22.
An dai shirya shi Badeh zai fara kare kan shi ne ranar 16 ga watan Janairu na wannan shekarar, amma kuma kafin ma lokacin ya yi, sai ‘yan bindiga suka harbe shi akan hanyar Keffi zuwa Abuja ranar 18 ga watan Disamba 18, 2018.
Lokacin da aka fara sauraren karar ranar 16 ga watan Janairu, wanda wannan kuma bayan mutuwar Bade, shi lauyan marigayin Chief Akin Olujinmi (SAN), wanda babban lauya ne na kasa, da kuma wanda yake kare Kamfanin Iyalikam’s, Mista Samuel Zibiri (SAN), wanda shima dai babban lauyan ne, sune suka roki shi mai shari’ar cewar a daga esauraren shari’ar har sai banyan an raufe shi marigayin Badeh.
Sun bayyana cewar idan aka yanke hukuncin wannan zai basu damar su samu cimma wani al’amarin, da shi mai gabatar da karar akan yadda za su ci gaba da yin ita shari’ar. Shi dai kamar yadda kowa ya sani tuni aka rufe shi.
Lokacin da aka ci gaba da sauraren ita karar ranar 26 ga watan 2019, lauyan da yake kare shi kamfanin ya bukaci da a sake dage sauraren shari’ar, saboda shi kamfanin aya samu dama wadda zai sake shiryawa mai shari’ar Abang ya amince da bukatar tasu har ya dage sauraren ita shari’ar har sai zuwa ranar litinin.
Ranar Litinin mai gabatar da masu laifi Mista Oluwaleke Atolagbe, ya bayyana ma Kotu cewar, wanda ake karewa da kuma mai karewar, ya bayyana ma kotu, sun cimma yarjejeniya, wadda zata kai ga sa a samu yin gyara, akan su laifukan guda goma, wanda kuma hakan ya sa aka cire sunan shi Badeha matsayin wanda ake karewa dangane da ita matsalar shari’ar.
Ya ci gaba da bayanin cewar, “Mun gabatar bukatar tamu ranar 4 ga watan Maris, bayan haka kuma mun gabatar da bukatar yarjejeniya da amincewa, wannan kuma idan aka yi la’akari da aka yi da tanaje- tanajen dokar tafiyar da al’amarin aikata laifi.”
Olujinmi wanda shi ne ya wakilci Badeh ya yin da and Mista S.T. Ologunorisa (SAN) shi kuma ya wakilci kamfanin Iyalikam Nigeria Limited, ranar Litinin anda kum ba wai an yi la’akari bane da da matakin Atolagbe, su zarge-zargen ko kuma tuhumce- tuhumcen bai kamata a karanta su a fili ba, saboda shio kamfanin baya da anda yake wakilatar shi a kotun .
Amma kuma sai Atolagbe ya dage cewar rashin wani wakilin kamfanin ba dabara bace wadda zata hana shi kamfanin ya amince da ya aikata laifin, a gaban kotun.
Ya ci gaba da bayanin gyaran dokar yadda ake tafiyar da shari’ar aikata laifi ta shekarar 2015, ta amince da shi al’amarin yarjejeniya da amincewa wadda tuni aka gabatar da ita a gaban kotun. Da yake shi mai shari’ar ya yi amfani ne da shawarar Atolagbe shi gyaran da aka yi an karanta ma kamfanin shi, bayannan kuma shi al’amarin da an amince an aikata, an dauki bayani ko maganar hakanan ma shi kamfanin, a madadin dukkan laifukan goma.
Da yake gabatar da hukuncin wanda ya amince da shi al’amarin na yarjejeniya da amincewa, wato maslahar da aka cimmawa, tsakanin shi wanda aka yi kara da kuma wanda yake karewa, mai shari’a Abang ya kama kamfanin da aikata laifi.
Ya ci gaba da bayanin cewar yanzu ga shi a gabana wata maganar sulhu wadda aka amincemawa tskanin kamfanin da kuma Hukumar EFCC. “Saboda haka na samu shi wannan kamfanin na Iyalikam Nigeria Limited da aikata laifi, hakannan ma su sauran laifukan goma, da kuma gyaran da aka yi.
“Da yake an amince da shi al’amarin yarjejeniya da amincewa wadanda masu nasaba da shi al’amarin duk suka sa hannu, don haka shi kamfani yanzu an rufe shi, bugu da kari kuma shi hukuncin da aka yanke za’a shaida da kuma aika ma Hukumar da take kula da rajistar kamfanoni (Corporate Affairs Commission) saboda ta dauki mataki na gba.”
Mai shari’a Abang bugu da kari ya bayar da umarni na duk wadansu kaddarori na kamfanin yanzu kuma sun zama mallakin gwamnatin tarayya. Daga karshe kuma shi mai shari’ar ya bada umarni ko kuma ya ce, an kawo karshen duk wata shari’ar data danganci shi Badeh.

Exit mobile version