Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta narkar da jimillar kudi na dala biliyan 9.76, wajen biyan bashi a tsakanin shekarar 2015 da shekarar 2020.
Rahoton CBN ya bayyana cewa, bashi ya lakume dala biliyan 1.3 a shekarar 2019, yayin da aka kashe dala biliyan 5.77 a shekarar 2020. Rahoton CBN ya ci gaba da cewa, dala biliyan 1.47 aka kashe wajen biyan bashi a shekarar 2018, sannan an kashe dala miliyan 444.77 a shekarar 2017. Gaba daya dai a tsakanin shekarar 2015 zuwa shekarar 2016, an kashe tsakanin dala 349.6 zuwa dala miliyan 378.91 wajen biyan bashi.
Binciken Babban Bankin ya nuna cewa, biyan bashi shi yake ci gaba da lakume kasafin kudin gwamnatin tarayya.
Rahoton ya nuna cewa, gwamnatin tarayya ta kashe jimillar dala miliyan 199.76 a wajen biyan bashi a shekarar 2019, yayin da ta kashe dala 4.43 wanda she ne mafi girman biyan bashin da aka biya a shekarar 2020.
Mataimakiyar gwamnan CBN ta bangaren tsare-tse kudade, Mista Aisha Ahmad ta bayyana cewa, sakamakon raguwar farashin mai ne ya janyo karancin samun haraji wanda ya tilasta cin bashi a cikin kasar nan.
“Akwai bukatar gudanar da wasu canje-canje wanda domin samun damar rage basuka da cike gibin kasafin kudi, wanda gwamnati ta kashe matukan kudade domin samar damar gudanar da tsare-tsaren tattalin ar ziki.”
Bankin raya yankunan Afirka ya bayyana cewa, biyan bashi shi ke lakume kashe 50 na kudaden harajin da Nijeriya ke samu. Bankin ya bayyana hakan ne lokacin gudanar da taron warware matsalolin tattalin arziki wanda ya gabata a makon jiya.
A cewar bankin, kasashen Yammacin Afirka suna biyan bashi wanda ya kai na kashi 17. Amma Nijeriya tana biyan na kashi 50 wajen biyan bashi. Wannan ya hada da bashin cikin gida da kuma na kasashen ketare.
Bankin ya ce, an samu karuwar yawan biyan bashi a Nijeriya da kashi 128, wanda ya lakume yawan kudaden harajin da Nijeriya take samu.
Ya ce, “duk da karuwar bashin da ake samu a Nijeriya na kashi 15.2, bai kai na sauran kasashe kamar irin su Benin da Guinea-Bissau da Togo wanda suke daa na kashi 25.
“Karuwar basuka yana janyo tarin matsaloli musamman ma a bangaren samun haraji. An dai samu karuwar biyan kudaden basuka wanda ba a taba samu ba tun a shekarar 2010.
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta kashe naira biliyan 604.19 a wajen biyan bashin cikin gida a tsakanin watan Yuli zuwa watan Satumbar shekarar 2020.
Rahoto hukumar NBS ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta biya kudaden bashi a watan ukun shekarar 2020, wanda ya kai na naira biliyan 97.64, yayin da ta kashe naira biliyan 43.63 a wata ukun shekarar 2019, sannan kan kashe naira biliyan 488.5 a tsakanin watan Yuli zuwa watan Satumbar shekarar 2020.
Hukumar NBS ta kara da cewa, ana bin jihohin Nijeriya da gwamnatin tarayya bashin naira tiriliyan 32.22 kwatankwacin dala biliyan 84 a ranar 30 ga watan Satumbar shekarar 2020.
A cewar hukumar NBS, bashin da ake bin gwamnatin tarayya na cikin gida da waje yana kara habaka, inda ake bin Nijeriya bashin kasashen ketare na naira tiriliyan 12.19 ko na kashi 37.82, yayin da basukan cikin gida ya kai na naira tiriliyan 20.04 ko na kashi 62.18.
Rahoton ya bayyana cewa, akwai bashin dala biliyan 16.74 wanda bashi ne a tsakanin kasashe biyu, sannan akwai bashin dala miliyan 502.38, wanda bashi ne na hadakan kasashe, akwai bashin bankin kasar China na dala biliyan 3.26, akwai na hadakan kasuwanci wanda ya kai na naira dala biliyan 11.17.
Sakamakon karuwar basuka ne a Nijeriya, Babban Bankin Nijeriya ya kafa kwamitin tsare-tsaren kudade, domin samun damar dakile bashi. Kwamitin ya bukaci gwamnatin tarayya ya dauki tsauraran mataki wajen magance basuka a Nijeriya da fadada hanyoyin samun haraji da kashe kudaden gwamnati ta hanyar da suka dace.
A shekarar 2015, lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amshi ragamar mulkin kasar nan a karo na farko, Nijeriya ta biya basuka wanda ya kai na dala biliyan 16.34. Zuwa shekarar 2018, an biya dala biliyan 13.74, yayin da aka biya dala biliyan 21.22 a shekarar 2019.
Ofishin kasafin kudi na tarayya ya bayar da rahoton cewa, a tsakiyar shekarar 2020, an biya bashin naira tiriliyan 1.1 wanda ya nuna an samu raguwar naira biliyan 234.04 wanda ya nuna na kashi 17.47 tun daga na naira tiriliyan 1.34 a tsakiyar wannan shekarar.
“An biya jimillar basukan cikin gida na naira biliyan 853.61, yayin da aka biya naira biliyan 251.76 a lokacin wannan kididdiga. Bambancin yan da ke tsakani ya kai na naira biliyan 83.06 ko na kashi 8.87 a tsakiyar shekarar.”