Gwamnatin Tarayya Ta Rabar Da Naira Biliyan 16.1 Ga Masana'antu 22 — Ministan Kudi
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Rabar Da Naira Biliyan 16.1 Ga Masana’antu 22 — Ministan Kudi

byKhalid Idris Doya and Sulaiman
9 months ago
Minista

Gwamnatin tarayyar ta ce, ta rabar da zunzurutun kudade har naira biliyan 16.1 ga masana’antu su 22 da suka kamata daga cikin naira biliyan 75 da gwamnatin ta ware domin ingantawa da bunkasa bangaren.

Kazalika, ta kuma ce a cikin kwana biyar kacal ta rabar da wani karin naira biliyan 3.5 ga wadanda suka ci gajiya su 11,000 daga tsarin tura kudi ga masu bukata ‘Consumer Credit Scheme’, wanda ke da burin cimma ‘yan Nijeriya miliyan 80 domin agaza musu.

Gwamnatin tarayya ta ce mutane miliyan 25 zuwa yanzu suka amfana da tsarin tura kudin kai tsaye ga masu cin gajiya.

Wannan bayanan sun fito ne daga bakin ministan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Wale Edun, wanda ya bayyana a Abuja yayin taron ‘yan kasa da masu ruwa da tsaki kan aiwatar da manufofin da shugaban kasa da ministoci suka gabatar a zangon karshe na 2024.

Ya ce, Nijeriya na bukatar zuba hannun jari na akalla dala biliyan 20 kowace shekara domin samun nasarar zuwa ga muradin inganta tattalin arziki da samun damar inganta matakin ci gaba zuwa kaso 6.3 nan da shekarar 2027.

Da yake sake nanata bukatar zuba hannun jari cikin gaggawa, Mista Edun ya shelanta irin tasirin da zuba hannun jari ke da shi ga jagorantar ci gaban tattalin arziki da bunkasarsa hadi da taimakawa wajen aiwatar da ayyukan raya kasa.

Edun ya ce, “A zahirin gaskiya muna matukar bukatar karin ci gaba. Samun karin dala biliyan 20 duk shekara shi ne burin da muke da shi don samar da ababen more rayuwa da kuma samar da kayan aikin noma.”

Bugu da kari, Edun ya danganta tsarin kasafin kudi da daidaiton farashin musayar kudade su ne za su taimaka wa Nijeriya ta samu janyo hankalin masu zuba hannun jari sosai.

Kazalika, ministan kudin ya ce akwai gayar bukatar amincewa da sabon kudirin garambawul ga haraji, wanda ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa za su amfana daga wannan kudirin gyaran harajin.

Ya roki ‘yan majalisun kasa da su toshe kunnuwansu kawai su amince da kudirin domin amfanunsa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Next Post
Sojoji Za Su Tabbatar Da Manoma Kashi 85 Sun Yi Noma Lafiya A Damina Mai Zuwa – Sanata Yari

Sojoji Za Su Tabbatar Da Manoma Kashi 85 Sun Yi Noma Lafiya A Damina Mai Zuwa - Sanata Yari

LABARAI MASU NASABA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version