Umar A Hunkuyi" />

Gwamnatin Tarayya Ta Samar Da Naira Miliyan 700 Kan Gyaran Makarantu A Binuwai

Babban daraktan kwamitin shugaban kasa kan tallafa wa wadanda hare-haren ta’addanci ya shafa, Farfesa Sunday Ochoche, ya bayyana cewa, kwamitin na shi ya kebe Naira milyan 700 domin gyara makarantun gwamnati da aka lalata a Jihar Benuwe. Ochoche, ya bayyana hakan ne jiya a garin Gbajumba, ta karamar hukumar Guma, lokacin da yake kaddamar da shirin sake ginawan, ya ce a kananan hukumomi uku na Jihar ne, Guma, Logo da Agatu, za a kaddamar da ayyukan.

Ya kuma bayyana cewa, za a sake gina cibiyoyi 28 ne sa’ilin da 23 daga cikin su duk makarantu ne, biyar kuma kananan asibitoci ne. Za kuma a kammala aikin ne a cikin watanni uku kamar yadda gwamnati ta dora wa kwamitin alhakin hakan.

A na shi jawabin, Gwamna Samuel Ortom, wanda mataimakinsa, Benson Abounu, ya wakilce shi, ya yi roko ne ga kwamitin da ya sake ginawa tare da sanya kayan aiki a cikin asibitocin, gwamnatin Jihar, shi kuma ya yi alkawarin wadata asibitocin da magunguna.

Ortom, ya kuma yaba wa kwamitin kan yadda ya amsa kiran da suka yi masa cikin hanzari, ya bayyana cewa, wakilan kwamitin sun sadaukar da rayukan su, suka ziyarci wuraren da abin ya shafa hatta a lokutan da ake ci gaba da kashe-kashen.

Exit mobile version