Idris Aliyu Daudawa" />

Gwamnatin Tarayya Ta Samu Gibin Naira Biliyan 977 A Shekarar 2017 — FRC

Gwamnatin tarayya ta samu haduwa da ci baya na Naira biliyan 977.57 wadanda aka kiyasta za a kashe a 2017, Hukumar rarraba kaddarori ta kasa ta bayana hakan.
Ita dai Hukumar ta bayyana hakan ne a wani rahoton data bayar a kan yadda aka aiwatar da kasafin kudi na shekarar 2017 wanda wakilinmu ya samu bayanan a Abuja ranar Litinin.
Kamar dai yadda ya bayar da rahoton Naira biliyan 977.57 sune wakilci bambanci na kudaden da za a kashe a kasafin kudi na 2017 da kuma ainihin kudaden da gwamnatin tarayya ta kashe.
Rahoton ya bayyana cewar, “Yawan kudaden da aka kiyasata a cikin kasafin kudin Naira Tiriliyan 7.44 idan aka hada da Naira Tiriliyan 6.46 wadanda aka kashe, wannan ya nuna an samu gibin Naira biliyan 977.57 ko kuma kashi 13.14.
“Yayin da kuma yawan kudaden da aka samu amatsayin kudaden shiga Naira Tiriliyan N5.08, a wannan an samau gibin Naira Tiriliyan 2.36, wannan kuma yawanci daga amsar bashi ne.”
Akan kuma yawancin abubuwan da shi kasafin kudin ya kunsa kamar yadda shi rahoton ya bayyana. “Gaba daya su kudaden da aka kashe a shekarar 2017 Naira Tiriliyan.17 wannan kuma shine ya kasance kashi 29.22 na kudaden da aka kiyasta wadanda maganarsu tafi su yawa, wannan kuma ya nuna ansamu karuwar Naira biliyan 587.1 k kuma kashi 36.98 a shekarar 2016 abin da ya shafi kassafin kudi, na Naira Tiriliyan1.59t ko kuma kashi 26.19 .
“Idan aka yi la’akari da yadda aka kashe kasafin kudin shekarar 2017 dama an yi kiyasin a duk watanni hudu za’a samu gibin Naira biliyan N589.19. Shi dama wannan gibin ana sa ran shi, saboda akwai wasu abubuwan da za’ ayi amfani dasu wajen maganin hakan wadanda suka kai Naira biliyan 2.5, ga kuma amso bashi daga kasashen wajen na Naira biliyan 266.88, sai kuma bashin cikin gida na Naira biliyan 313.57, ga kuma sayar da wasu kaddarorin gwamnati na Naira biliyan 25.
“Sai kuma ai ka ma wasu Hukumomin da aka yin a shi kasafin kudin abin da ya kai ga Naira biliyan 434.41 yayin da kuma Naira Tiriliyan N1.66 an ware sune saboda biyan basussuka N177.46, sai kuma al’amarin wasu kudade wadanda suka samu matsala Naira biliyan 2.99.
“Amma duk da hakan akwai jimillar Naira biliyan 434.41 su an kashe sune a shekarar 2017. Wannan shine ya ke nuna kashi 100 na kudaden da aka kashe a kasafin kudin.
“Yana da kyau a gane cewar yawan kudaden da ake sakarwa duk wata hudu, ga wadanda suka kamata, wannan kuma ya danganta ne ga idan da akwai kudaden. Wannan ya nuna bambancin akan su kuadaen wadanda aka kashe duk bayan watanni hudu na yadda ake kashe shi kasafin kudin.”
Hukumar FRC ta bayyana cewar amfani yadda ake bin diddikin yadda ake kashe kudaden kasafin kudi, ya yin da kuma ita dokar Hukumar, ita ce wadda take fuskantar matsala,wannan kuma yana kasancewa ne saboda yawancin su Ma’aikatu da kuma Hukumomi sai wasu sassan gwamnati basu ba ita Hukumar hadin kai wajen tafiyar da ayyukanta.

Exit mobile version