Yusuf Shuaibu" />

Gwamnatin Tarayya Ta Samu Harajin Naira Biliyan 881.02 Daga Cibiyoyin Kudade A Shekaru Biyar

Shigo Da Mai

Gwamnatin tarayya ta karkashin hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS), ta samu harajin naira biliyan 881.02, daga harajin kamfanoni da kuma harajin kayayyaki a wajen cibiyoyin kudade da ke Nijeriya a shekaru biyar. Ta dai samu kashi 30 daga cikin harajin kamfanoni wanda ya kai naira miliyan 100, wanda aka samu daga harajin rabar asasun karshen shekara. A shekarar 2020, gwamnatin tarayya ta kara harajin kayayyaki na kashi biyar daga kashi 7.5, domin gwamnati ta samu kudaden shiga daga bangarori wanda ba na mai ba.

Bankunan da ke cikin kasar nan suna biyan harajin kamfanoni da harajin ilimi da harajin ‘yan sanda da kayayyaki karin harajin. A cikin rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ya kididdiga yawan harajin naira 881.02 wanda hukumar FIRS ta samu daga cikin harajin kamfanoni da kayayyaki. Rahoton ya nuna cewa, an samu harajin naira biliyan 121.17 a shekarar 2020, kusan kashi 24 daga cikin rahoton harajin da aka samu a shekarar 2019 na naira biliyan 159.85. A shekarar 2018, hukumar FIRS ta tattara harajin naira biliyan 158.58 wanda aka samu ta hanyar harajin kamfanoni da harajin kayayyaki wanda ya zarce na naira biliyan 148.96. Sannan an samu harajin naira biliyan 133.99 a shekarar 2015.
Da yake bayanin yadda aka samu harajin kamfanoni da harajin kayayyaki na bankuna da sauran cibiyoyin kudade a shekarar 2020, masanin tsare-tsaren kudade kuma shugaban masu amsar harajin bakin teku a yankunan Afirka, Mista Taiwo Oyedele ya bayyana wa manema labarai cewa, “yana da matukar mahimmanci mu fahimci tsarin ayyukan harajin, domin idan ba haka ba zamu dunga samun rudani, bunkuna sun sami kudade masu yawa a shekarar 2020, amma sun biya haraji dan kadan wanda hakan ba dai-dai ba ne.
“Abin da ya faru dai shi ne, an amshi harajin shekarar 2019 a shekarar 2020 wanda a yanzu aka sake bibiyan lamarin. A cikin wannan gyara da muka yi mun samu mahimman mataki da muka dauka.
“Harajin da aka biya a shekarar 2020, riba ne na shekarar 2019 wanda ba a samu biya ba har sai a shekarar 2020. Bankuna sun sami kudade masu yawa a lokacin cutar Korona. Za a sami harajin ne a wannan shekarar ta 2021.
“A bangaren harajin kayayyaki kuwa, an dai cira kananan bankuna daga cikin bayan haraji tun a karshen shekarar 2019. Idan muka hada tasirin yin haka, ina tunanin wannan shi ne aka samu a cikin harajin kamfanoni da harajin kayayya a shekarar 2020.
“Ko kafin cutar Korona, akwai da yawan bankuna da ba sa samun riba. Wadanda suna samu kudade masu yawa a shekarar 2020 su ne wadanda suke da kayayyain kimiyya da yawa. Ba na tunanin matsalar na rashin samun riba ne.
“Ko sun sami riba a shekarar 2020, ko ba su samu ba a rahajin da za a gani ba ne a shekarar 2020, wanda za a gani ne a shekarar 2021,” in ji shi.
Da yake gabatar da jawabi, shugaban cibiyar haraji ta Nijeriya Dame Gladys Simplice ya bayyana cewa, an samu harajin kamfanoni da kayayyaki wanda bankuna da sauran cibiyoyin kudade a lokacin dokar takaita zirga- zirga ya kai na kashi 24.
Ya ce, “harkokin kasuwanci ba sa gudana a wannan lokaci, amma an samu haraji mai yawa daga bankuna.
“Alal misali, kamfanoni sun sami karancin gudanar da harkokin kasuwancinsu lokacin dokar hana zirga- zirga. Ba a rufe kamfanoni ba gaba daya, suna gudanar da kasuwancinsu amma ba sosai ba. Takaituwar harkokin kudade ya sa an sami karancin harajin kamfanoni da harajin kayayyaki a shekarar 2020.”
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da kamfanoni ta Jihar Legas, LCCI), Mista Muda Yusuf ya bayyana cewa, an sami matsaloli a cikin harkokin kasuwanci. Ya kara da cewa, bankuna bankuna sun sami riba amma sun biya gwamnatin tarayya harajin kamfanoni da harajin kayayyaki dan kadan a shekarar 2020.
A cewarsa, “bankuna da sauran cibiyoyin kudade sun biya harajin kamfanoni da kayayyaki ne dan kadan a shekarar 2020, sakamakon matsalolin tattalin ar ziki.”

Exit mobile version