Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Tarayya Ta Shigar Da ’Yan Bautar Kasa Cikin Tsarin NHIS

Published

on

A ranar Talata ne Hukumar NYSC ta sanar da cewa, gwamnatin tarayya a amince da shigar da matasa ‘yan bautar kasa a cikin tsarin inshorar kiwon lafiya ta kasa NHIS.

Brigediya Janar Suleman Kazaure, shugaban hukumar NYSC ya bayyana wa ‘yan jarida a yayin gudanar da bikin bude taron shekara shrkara na hukumar da bikin cikar hukumar shekara 45 da kafawa da aka gudanar a garin Akure.

Janar Kazaure ya kara da cewa, hukumarsa ta fara tattaunawa da wasu asibitocin gwamnatin tarayya a kan yadda za su taimakawa masu bautar kasa shiga shirin na inshorar lafiya don su samu daman samun ingantaccen kiwon lafiya a duk inda suke a fadin kasar nan.

Ya ce, duk da cewa, an kafa tsarin NYSC ne don hada kan kasa da kuma hada kan ‘yan kasa gaba daya ya kuma zama dole a nemi izinin gwamnatin tarayya don shigar da masu bautar kasar a cikin shirin NHIS wadda aka kafa a shekarar 2014 don bayar da ingantaccen kiwon lafiya ga ‘yan Nijeriya gaba daya.

“Gwamnatin tarayya ta amince da a sanya dukkan masu bautar kasa a cikin tsarin NHIS, a halin yanzu komai ya na tafiya a cikin tsari babu matsala.

“Mun riga mun fara shirin hadin kai da ma’aikatar lafiya da kuma asibitocin gwamnatin tarayya don bayar da cikaken kiwon lafiya ga masu yi wa kasa hidima ta hanyar samar da cikkaken kwararen likita daga manyan asibitin kasar nan a dukkan  sansanin horar da masu yi wa kasa hidimar dake a fadin tarayyar kasar nan,” inji shi.

Ya kuma kara da cewa, shirin ya samu nasarar kammala cibiyar koyar da sana’o’i a na yankin kudu maso yammacin kasar nan da aka gina a garin Iyin-Ekiti, ta jihar Ekiti, duk a karkashin zamanin jagorancinsa na shugabancin hukumar.

“Wasu nasarorin da aka samu a zamanin mulkinsa sun hada amfani da fasahar kwamfuta wajen gudanar da ayyukan hukumar da kuma tanadar kujerun guragu don amfanin masu yi wa kasar hudimar a sansanin horar dasu da kuma shirin kawo dauki ga na kiwon lafiya ga ‘yan yankunan karkara,’

Ya kuma bayyana cewa, wanna taron da ake gudanarwa shekara shekara ana tattara manyan ma’aikatan hukumar don su tattauna yadda za a ciyar da harkar hukumar gaba, ta hanyar fito da tsare tsare masu amfani.

Da yake jawabin bude taron, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce, shirin NYSC ya bayar da gudummawa matuka wajen bunkasa ci gaban kasa da harkar dimokradiyya.

Gwamnan wanda mataimakinsa, Mista Agboola Ajayi, ya ce, NYSC na bayar da gudummawa matuka ga rayuwar jama’ar kasar nan, ya kuma kara da cewa, NYSC ya bayar da gudumawar kasha 80 a wajen ci gaban starin dimokradiyyar kasar nan gaba daya.

“Bayan hada kan ‘yan kasa, NYSC  ya kuma rage kysamar juna a tsakanin ‘yan Nijeriya tare da kuma karfafa hadin kai a tsakannin ‘yan Nijeriya da kuma fahintar juna a dukkan lokutta”

I taimaka matuka wajen sake wa shirinb alkibla da kuma karfin sake fuskantar gaggarumin aikin dake a gabansu na ciyar da hukumar gaba..

“A namu gudummwar don ganin hukumar ta samu nasarar a harkokinta, gwamnatinmu za ta samar da kyautar Naira 100,000 da naira 80,000 da kuma naira 50,000 don karrama masu bauta wa kasa da suka yi bajimta,’ inji ta.

Tun da farko, shugaban gudanarwa na hukumar ta NYSC, Fatima Abubakar, ta ce, taken taron na wannna shekarar ya yi dai dai da tsarin gwamnatin tarayya na samarb da wasu hanyoyi don bunkaa tattalin arzikin kasar nan ta hanyar ba matasa dammar da ya kamata.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: