Abubakar Abba" />

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Samar Da Yanayin Gudanar Da Aiki A Cikin Jin Dadi

Gwamnatin tarayya ta bayana cewar, a shiye take wajen samar sa kyakyawan yanayin gudanar da aikin gwamnati kamar yadda dokar kwadago ta kasa da kasa ta tanadar.

Babban Sakatare a ma’aikatar kwadago ta tarayya Mista William Alo be ya bayyana hakan a Abuja a lokacin da ya karbi bakuncin Hukumar mata ta kasa NWC sake a karkashin kungiyar kwadago ta kasa don amincewa da  yarjejeniyar da aka comma ta kasa da kasa ta ILO don kare cin zarafin mata a Turin aiki.

Mista William Alo ya ci gaba da cewa, Nijeriya tana yin kokarin wajen kiyaye nunawa mata ban-banci a guraren da suke gudanar da ayyukan su, inda ta samar da wadatattun dokoki don basu kariya.

Acewar Mista William Alo, idan aka samar da kyakyawan yanayin da ya dace, zai samar da ma’aikatan zaman lafiya, soyayya da juna da kuma fahimtar juna, inda ya ce, wannan kokarin na wayar da kai da akeyi akan samar da kyakyawan yanayin yazo a daidai kan gaba.

Ya samar da kokarin da gwamnatin take yi wajen bayar da goyon bayan ta akan yarjejeniyar ta ILO na baiwa mata ma’aikata Mariya a guraren da suke gudanar da ayyukan su, musamman don kara ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba.

Mista Williams Alo ya kuma taya ma’aikatan kasar nan da kuma kungiyar kwadago NLC akan kokarin da suka yi na samar da sabon karin mafi karancin albashin kananan ma’aikata, inda ya yi nuni da cewa, gwamnatin akoda yaushe tana son taga ta na farantawa ma’aikata.

Babban Sakataren ya kuma nuns jin dkdinsa akan yadda kungiyar kwadago ta kasa take baiwa ma’aikatar hadin kai akan lamurran da suka shafi kwadago musammanndon a farantawa ma’aikata rai.

A nata jawabin tunda farko, Mercy  Okezie wadda ta jagorance tawagar Hukumar  ta ce Hukumar tazo ma’aikatar ce don neman goyon bayan ta domin amincewa da dokar ta kwadago ta kasa da kasa don a daina nunawa mata wariya da tsangwamar su a guraren gudanar da ayyukan su.

Ta bukaci a amince da yarjejeniyar da aka cimma ta dokar ta  ILO don a daina nunawa mata dukkan wasu nau’uka na tsangwama da wariya a guraren da suke gudanar da ayyukan su.

Exit mobile version