Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan N9.6 Don Biyan Ma'aikata Kuɗaɗen Inshorar Rayuka
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan N9.6 Don Biyan Ma’aikata Kuɗaɗen Inshorar Rayuka

bySulaiman
2 years ago
Amurka

Shugaba Bola Tinubu ya amince da ware Naira biliyan N9.6 a wannan shekara domin sabunta biyan inshorar rayuka na ma’aikata a ƙarƙashin Group Life Assurance.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ne ya bayyana haka a ranar Laraba, bayan kammala Taron Majalisar.

  • Yawaitar Hadurran Mota A Hanyoyin Kasar Nan
  • Minista Kyari, Gwamna Nasir Sun Kaddamar da Shirin Noma Na KADAGE A Kebbi

Da ya ke magana da manema labarai bayan kammala taron a Fadar Shugaban Ƙasa, Idris ya ce an amince da kuɗaɗen ne biyo bayan wata takarda da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan ta gabatar a wurin taron.

A taron wanda shi ne na farko cikin 2024, Minista Idris ya ce za a biya kuɗaɗen a ƙarƙashin kamfanonin inshora 12 na cikin gida, domin biyan inshorar ma’aikatan da wani Ibtila’i ka iya faɗa masu a lokacin da suke kan aikin su.

“Akwai aƙalla kamfanoni 12 da za a riƙa biyan inshorar a ƙarƙashin su. Kuɗaɗe ne da aka saba bayarwa duk shekara, waɗanda kamfanonin inshora ke bayarwa ga ma’aikata.

“Saboda haka idan mutuwa ta riski wani ma’aikaci ko ibtila’i ya same shi har ya samu rauni, to waɗannan kuɗaɗe za a biya ga iyalin sa, don kada su yi fama da jidalin zaman ƙunci,” cewar ministan.

Idris ya ce Shugaba Tinubu ya amince da biyan kuɗaɗen saboda kyakkyawan muradin wannan gwamnati na inganta jin daɗin ma’aikata, domin su ƙara ƙwazo wajen yi wa ƙasar su aiki da gaskiya kuma tuƙuru.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
Siyasa

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Next Post
DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Tsige Gwamnan Nasarawa Na APC Ta Ayyana Umbugadu Na PDP

Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Zaɓen Sule A Matsayin Gwamnan Nasarawa

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version