Gwamnatin Tarayya Ta Yi Tir Da Yadda Gwamnatin Zamfara Ke Siyasantar Da Matsalar Tsaro
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Tir Da Yadda Gwamnatin Zamfara Ke Siyasantar da Matsalar Tsaro

bySulaiman
2 years ago
Gwamnatin tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana matuƙar damuwa kan wata sanarwa da ta fito daga Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Dauda Lawal Dare.

Gwamnatin ta ce maimakon gwamnan ya nuna jin daɗi da farin ciki ganin yadda jami’an tsaro da hukumomin Gwamnatin Tarayya ke ta ƙoƙarin ganin an ceto ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Gusau daga hannun ‘yan bindiga, sai ya maida matsalar siyasa don kawai ya cimma wani buri a siyasance.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Zargin Tattaunawa Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
  • Bukukuwan Maulidi: Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Ranar Haihuwar Fiyayyen Halitta.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka bayan ya nazarci yadda dokar ƙasa ta bai wa hukumomin Gwamnatin Tarayya ƙarfin ikon zabura domin ɗaukar matakan tabbatar da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, kamar irin yadda aka yi wa ɗaliban Jami’ar Tarayya ta Gusau.

A cewar sa, don hukumomin da aikin ceton ɗaliban ba su fito sun sanar da irin ayyukan ceto ɗaliban ba, hakan ba ya nufin ana wata ƙumbiya-ƙumbiya kamar yadda gwamnan Zamfara ya yi wa ƙoƙarin da ake yi karkatacciyar fahimta.

A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai a Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Suleiman Haruna, ya rattaba wa hannu, ministan ya bayyana cewa babu wani jami’in Gwamnatin Tarayya wanda ke tattaunawar sulhu da wani ko wasu gungun ‘yan bindiga.

Ya ce ita Gwamnatin Tarayya ta na nan kan matsayar ta ta tabbatar da bin duk wasu hanyoyin da su ka dace, waɗanda binsu zai tabbatar da an daƙile tashin hankula kuma an dawo da zaman lafiya a cikin jama’a.

Sai dai kuma ya ce, idan jama’ar wasu yankuna su ka yi tunanin ɗaukar irin matakan da wasu yankuna su ka ɗauka har su ka kashe fitilar tashe-tashen hankula, ta hanyar neman sasantawa, to Gwamnatin Tarayya ba za ta yi gaggawar taka masu burki ko yi wa shirin nasu Allah-wadai ba.

Idris ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomin ta na aiki haiƙan don kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da duk wasu ayyukan laifuffuka.

Daga ƙarshe, ministan ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya za ta saurari shawarwarin dukkan masu wani tasiri domin ƙoƙarin samun hanyoyin da za a bi a kawo ƙarshen matsalolin tsaro.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Manchester City

Newcastle Ta Kori Manchester City A Gasar League Cup Ta Kasar Ingila

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version