Umar A Hunkuyi" />

Halin Da Ake Ciki Game Da Dakile Bazuwar COVID-19 A Jihohin Arewa

Cutar sarkewar numfashi da aka yi wa lakabi da COVID-19 ta haifar da gagarumar barazana ga rayuka har ma da dukiyoyin al’ummar duniya bakidaya, inda a yanzu haka kusan za a iya cewa cutar ta zama ruwan dare game da duniya.
Da yake tun barkewar cutar a yankin Wuhan na kasar Sin a karshen watan Disambar 2019, gwamnatoci da dama sun dukufa ga daukar matakai domin kiyaye al’ummominsu, LEADERSHIP A YAU JUMA’A ta shirya rahoto na musamman a kan irin matakan da Jihohin Arewa ke dauka domin dakike bazuwar cutar a tsakanin al’ummominsu. Inda muka kawo muku rahotannin daki-daki tare da bayyana halin da jama’a ke ciki a jihohin.
Sai dai za mu fara da bangaren tarayya, domin jin irin halin da ake ciki game da yaki da cutar da Gwamnatin Tarayya ke yi, kamar haka:

…Gwamnatin Tarayya Tana Neman Mutum 4,370, Masu Alaka Da COVID-19

Gwamnatin tarayya ta ce har yanzun tana kan neman zakulo mutane 4,370 da suka yi wata alaka da masu dauke da cutar COVID-19. Kana ya ce akwai yiwuwar a tsaurara matakan da ake dauka yanzu haka.
Gwamnatin ta bayyana takaicinta a kan yanda yawancin mutanan da suke komowa daga kasashen waje ba sa bayar da adireshinsu na gaskiya.
Gwamnatin ta kuma ce sabanin abin da ake yadawa musamman a kafofin yada labarai na yanar gizo, Shugaba Muhammadu Buhari, ba wani tarin da yake yi a bayan da aka gwada shi aka kuma tabbatar da cewa ba ya tare da cutar ta Koronabairus.
Gwamnatin ta ce Shugaban kasan yana nan daram da karfinsa, a shirye yake kuma ya ci gaba da gudanar da aikin da ya hau kansa na shugabancin kasar nan.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan a wani taron bayarda bahasin halin da ake ciki dangane da cutar ta COVID-19.
Ministan ya ce: “Akwai mutane 4,370 da muke da bukatar mu nemo su. Muna kuma bukatar duk wanda ya san ya yi wata alaka da wadanda ake tuhumar yana dauke da cutar da su hanzarta kai kansu ga hukumomi. Muna kuma bukatar dukkanin ‘yan Nijeriya da su bai wa hukumomi goyon baya a kan hakan.
Ministan ya ce, gwamnati tana cikin damuwa a bisa yanda wasu masu komowa daga kasashen waje ba sa bayar da adireshinsu na gaskiya.
“Bari na shaida maku ba tare da wata tantama ba, sam ba fa ma samun goyon baya da hadin kan da ya kamata daga ‘yan Nijeriya. Da yawan mutanan kasar nan sun shagaltu ne da yin soke-soke a maimakon su bi dokan da aka shimfida domin zaman lafiyan al’umma.
“Wasu daga cikin ‘yan Nijeriyan da suke komowa cikin kasar nan daga kasashen waje suna bayar da adireshin karya da kuma lambar waya ta karya ne a cikin takardun da suke cikewa, wanda hakan ya sanya yana da wuya a iya gano su in bukatar hakan ta taso.
“Wasu ‘yan Nijeriyan sun ki su bi dokar nisanta wuraren tarukan jama’a, a lokacin kuma da wasu shugabannin addinin suka yi kunnin uwar-shegu da dokar ta nisantar juna.
“Gwamnati tana yin bakin kokarinta, amma kuma muna da bukatar al’umma su ma su yi na su bakin kokarin.
Dangane da ainihin halin da Shugaban kasa yake a ciki kuwa, Ministan ya ce yana da tabbacin Shugaban kasan yana cikin koshin lafiya, a shirye kuma yake ya ci gaba da gudanar da mulkin kasar nan.
“Wasu na yada cewa wai Shugaban kasan yana ta fama da tari, wanda wannan labarin kanzon kurege ne.”

Exit mobile version