Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dakta Isa Ali Pantami, ya yi ganawa da shuwagabannin ma’aikatan hukumar kula da katin zaman dan kasa (NIMC), wanda ya amince da bai wa ma’aikataan albashi na musamman bisa karin ayyukan da aka yi musu. Sannan an tattauna sake sabon tsarin biyan ma’aikata da karin girma da kuma biyan sauran hakkokinsu. Pantami ya bukaci hukumar da ta kafa kwamiti na musamman wanda zai bibiyi yadda za a biya albashin na musamman da kuma sauran hakkokin ma’aikatan.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani Dakta, Isa Pantami ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tana gudanar da kokari wajen tabbatar da ganin hukumar NIMC ta tsaya da kafafuwanta.
Ya ce, “burin da nake da shi a yanzu shi ne, tabbatar da cewa hukumar NIMC tana samun kudaden shiga da kanta wajen gudanar da ayyukanta ba tare da ta jira kasafi ba daga asusun gwamnatin tarayya.
“Hukumar NIMC yana da matukar mahimmanci wajen bunkasa ci gaban Nijeriya. Zai yi amfani da matsayina na minister wajen bunkasa hukumar,” in ji Pantami.
Gwamnatin tarayya ta bai wa ma’aikatan hukumar wa’adin ranar Jumm’a, 29 ga watan Junairu dukkanin bukatocinsu da kuma sauran abubuwan da suke bukata na gudanar da ayyukansu. Ma’aikatan suna fuskantar rashin isasshen kamfutoci a shalkwatan hukumar da sauran rassan hukumar wanda hakan ke haihar da tsaiko wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Ma’aikatan hukumar NIMC sun roki gwamnatin tarayya da ta yi kokarin cika musu korafe-korafen da suka mika mata domin samun gudanar da ayyukansu yadda ya dace.