Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Gidaje 10,000 A Borno – Sadiya Farouk

Published

on

Minista a ma’aikatar bayar da agajin gaggawa da tallafa wa wadanda ibtila’i ya shafa, Hajiya Sadiya Farouk, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta kashe kimanin naira biliyan 20 domin gina gidaje 10,000 a jihar Borno.

Ministar ta sanar da hakan ne karshen wannan makon, a sa’ilin da take jawabi a taron kaddamar da dora harsashen aikin gina sabbin gidajen, a kauyen Ngom, da ke wajen birnin Maiduguri, inda ta kara da cewa za a raba wadannan gidaje 10, 000 ga yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya shafa, kana kuma wadanda ke zaune a matsugunan yan hijira daban-daban.

Haka kuma ta bayyana cewa, “Wannan shi ne kaso na farko na gina wadannan gidajen, wadanda gwamnatin tarayya za ta gina a nan jihar Borno, domin raba su ga yan gudun hijira. Wanda za mu fara da wannan kauye ta hanyar gina gidaje 1,000 tare da gina sauran zuwa kananan hukumomi 10 da ke fadn jihar Borno,” in ji ta.

A nashi bangaren kuma, babban Daraktan hukumar sake raya yankin arewa maso gabas (NEDC), Alhaji Mohammed Alkali ya bayyana cewa ayyukan wadannan gidajen zai taimaka wajen rage karancin gidajen da ake dasu a yankin, biyo bayan barnar da mayakan Boko Haram su ka tabka wajen kona gidajen jama’ar arewa maso gabas.

“Jihar Borno kadai ta yi asarar gidaje sama da kaso 60 cikin dari na adadin gidajen da ake dasu a jihar. Yayin da saboda yadda aka samu wannan gibi, ya jawo shugaban kasa, Mohammadu Buhari ya amince da gina gidaje 10,000 a jihar Borno.” In ji shi.

Bugu da kari kuma, ya bukaci gwamnati ta dauki matakin samar da ci gaba ta hanyar sake gina-gine da gyara-gyaren wuraren da matsalar ta barnata tare da matakan yakin da fatara a yankin Arewa maso Gabas.

Ya ce, akwai kimanin mutum miliyan uku da su ka tsere daga gidajen su ta dalilin hare-haren mayakan Boko Haram, wadanda kuma ke ci gaba da rayuwa a sansanonin yan gudun hijira. Sannan daga cikin wannan adadin, jihar Borno ce abin ya fi shafa kana da yan gudun hijirar da yawan su ya doshi miliyan 1.8, a kididdigar da hukumar kula da yan gudun hijira ta majilisar dinkin duniya (OCHA) ta bayar a shekarar 2019.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: