Ranar Litinin Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kai wa ministan ilimi na Nijeriya Malam Adamu
Adamu ziyara tare da godiya, biyo bayan amincewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari na gina sabuwar kwalejin kimiyya (Federal Polytechnic) a Monguno, gari mafi yawan jama’a a arewacin jihar Borno, wanda kuma ya dade yana fuskantar koma bayan ilimin boko.
Kafin hakan, yau kimanin shekaru 45 da kirkiro jihar Borno (1976), tun a wannan lokacin jihar ta ci gaba da kasancewa daga cikin jihohin yan kadan da basu mallaki kwalejin kimiyya ko kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya ba a fadin kasar nan.
Bugu da kari, kwalejin kimiyya ta Ramat da ke Maiduguri, gwamnatin jihar Borno ce ta gunata kuma take gudanar da ita, wadda a baya jihar ta yi kokarin gwamnatin tarayya ta karbi Ramat Polytechnic amma abin ya ci tura.
Har wala yau kuma, mafi yawan jihohi 36 da ke fadin Nijeriya, kusan kowace za ka tarar tana da daya daga cikin biyun nan- akallah ka sameta da Jami’ar gwamnatin tarayya ko kwalejin kimiyya tare da kwalejin ilimi. Amma ita jihar Borno yau kimanin shekaru 45 da kirkirota amma ba tada ko daya daga dikin wadannan manyan makarantun tarayya, alhalin wasu jihohi da dama da aka kirkiro bayan ta su na kusan duka ukun.
Saboda wannan haki na jihar Borno ya jawo Gwamna Zulum, a matsayin sa na malamin jami’a kuma tsohon shugaban Ramat Polytechnic, ya tashi tsaye haikan wajen bin bayan wannan matsala a wajen gwamnatin tarayya domin gina sabbin kwalejin kimiyya da kwalejin ilimi a jihar Borno, duk da halin da ake ciki ta matsalar rikicin Boko Haram, wadda za a gina a arewacin jihar.
Wanda bisa ga hakan ne Farfesa Zulum ya bayyana farincikin sa a sa’ilin ziyarar da ya kaiwa ministan ilimin a sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja. Yayin da ya yaba wa gwamnatin shugaban kasa Buhari dangane da amincewa da gina sabuwar kwalejin tare da bika dimbin godiya ga ministan ilimi Malam Adamu Adamu bisa tabbatar da umurnin da nuna kauna ga al’ummar jihar Borno.
A nashi bangaren, minista Adamu ya sanar wa Gwamna Zulum cewa baya ga gina sabuwar kwalejin kimiyya, nan kusa kuma Borno za ta samu karin kwalejin ilimi kamar yadda yake a mafi yawan jihohin kasar nan 36.