Muhammad Maitela" />

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ginawa ‘Yan Gudun Hijira Gida 10,000 A Borno – Zulum

‘Yan Gudun Hijira

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa gwamnatin tarayyar Nijeriya ta fitar da Naira bilyan 5. 2 domin gina gidaje ga al’ummar da rikicin Boko Haram ya shafa a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan a sa’ilin da yake rangadin aikin ginin rukunin gidaje 1, 000 domin yan gudun hijirar jihar wadanda gwamnatin jihar ke aikin mayar dasu garuruwan su, a kauyukan da ke kusa da birnin Maiduguri, inda ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta fitar da wadannan kudin saboda gina gidaje 10, 000 domin bayar dasu ga yan gudun hijira miliyan 1. 7 wadanda ake sa ran komawar su yankunan su.

A hannu guda kuma, wadannan yan gudun hijira, wadanda suka koma garuruwan su, suna zaune ne a matsugunan yan hijira a Maiduguri, Dikwa, Monguno, Dolori hadi da guda uku dake zaune a kan iyakar Nijeriya da jamhuriyar Kamaru.

Dangane da hakan, Gwamna Zulum ya sanar da cewa fitar da kudaden ya zo ne biyo bayan bukatar da gwamnatin jihar ta yi bara, a kudurinta wajen gina rukunin gidajen.

Exit mobile version