Daga Zubairu M Lawal,
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta amince da gudanar da allurar Rigakafi ga yara kanana da yawansu ya kai kimanin miliyoyin 23 daga jihohin arewacin Nijeriya.
Hukumomin kula da kiwon lafiya ta Duniya da su ka hada da WHO, SNIPD da OPB sun tabbatar da gudanar da allurar Rigakafin zai samar da kuzarin karin lafiya ga yara kanana.
Babban jami’i a ma’aikatan kiwon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Dakata Walter Kazadi Mulombo, ya ce gudanar da allurar Rigakafin zai taimakawa yara wajen samaun kariya daga cututtukar Shan-inna da Annobar cutar Korona bairus da sauransu.
Yin Allurar zai taimaka wajen kariya daga cutar Korona da bakon dauro da kyanda da sauransu.
Za a gudanar da allurar ne ga raya kanana masu matsakaicin shekaru daga ranar haihuwa zuwa wata 59.
Za a gudanar da rigakafin ne a jihohin Bauchi Borno Jigarawa Kaduna Kano Katsina Kwara Niger Sokoto Yobe da Jihar Zamfara.
A baya hukumar kiwon lafiya ta Nijeriya tayi nasarar magance matsalar cutar shan-inna. Yanzu za ta yi tsayin daka wajen kawar da cututuka masu yaduwa.
An dai fara gudanar da allurar Rigakafin a jihar Yobe inda aka gudanar a garuruwan Fika da Dogo dake yankin Patiskum an gudanar da gangamin yekuwa inda aka rika zuwa da yara ana masu allurar.
Taron ya samu halartan masu unguwanni da Dakatai da Hardodin Fulani da Shugabannin addinai da sauran su.
Malam Maryam Haruna ta samu nasara inda akayiwa yaranta ta ce a baya cutar Korona ya taba kama yarta ta sha wahala sosai.
Za a gudanar da allurar a Asibitocin sha-ka tafi dake karkara da biranai. Muhammad Lawan Gana Kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Yobe ya ce al’umman jihar sun ba da hadin kai wajen gudanar da allurar Rigakafin Kuma zasu bi birni da kauye zasu yi amfani da Sarakunan Gargajiya da Shugabannin addinai dana al’umma wajen wayar da kan mutane kan allurar rigakafin.