Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin daukar matasa 17,000 a daukacin fadin kasar domin ba su horo kan kiwon Zomo.
Babban Sakatare na hukumar Aikin Noma ta (NALDA) Paul Ikonne ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a a babban birnin tarayyar Abuja, inda ya kara da cewa, hukumar ta kuma tsara wani aiki domin daukar matsa a Kudancin kasar domin ba su horon kan kiwon Zomo.
A cewar Paul Ikonne, wadanda za su amfana ba ba wai kawai za a ba su horo da rage ma su zaman kashe wando ba ne kawai, za a kuma koya ma su yadda za su sarrafa kashi da fitsarin zomayen yadda za su sarrafa su zuwa takin zamani, Inda hakan zai ba su damar samar wa da kawunansu kudin shiga har naira 100,000 a duk wata.
Babban Sakatare na hukumar Aikin Noma ta (NALDA) Paul Ikonne ne ya bayyana cewa, kashi na farko na horon tuni aka fara gudanar da shi a jihohin Abia, Imo da kuma Oyo, inda ya kara da cewa, za kuma wanzar da aikin a daukacin jihohi 18 da ke a fanin kasar.
Babban Sakatare na hukumar Aikin Noma ta (NALDA) Paul Ikonne, Ikonne ya ci gaba da cewa, a karshen wata matasan za su samu kudin shiga daidai da yawan litar fitsarin na zomon da kuma kashin su bayan sun kai wa ofis-ofis na hukumar.
Paul Ikonne ya bayyana cewa, hukumar ta NALDA tuni ta fara wanzar da shirin a jihohi 18 da ne a fadin kasar nan, Inda aka bai wa jami’an hukumar da me a jihohin domin rabawa wadanda su ka amafana da horon, musamman a jihohin Oyo, Abia da kuma Koros Riba.
Babban Sakatare na hukumar Aikin Noma ta NALDA Paul Ikonne ya bayyana cewa, bayan horon matasan za a ba su zomo hurhudu ko wannensu wadanda za a sa ran za su kiwata su har zuwa tsawon watanni hudu.
A cewar Babban Sakatare na hukumar Aikin Noma ta (NALDA) Paul Ikonne, gwamantin za ta rabar wa da matsan da suka amfana zomoyen, abincinsu, magungunansu da kuma kejinan yin kiwon zomayen, inda kuma za a dauki wasu daga cikin yayan zomayen da aka haifa don a rabawar da sauran matsana da basu amafana ba domin su ma su fara yin kiwonsu.
A wani labarin kuwa, Ma’aikatar Noma da Raya karkara ta Tarayya ta dauki kwarran matakai don dakile matsalar karancin abinci a kasar nan.
Mai ba da shawara kan fasaha ga Ministan Noma kan Gudanar da Ilimi da Sadarwa Barista Richard Mark Mbaram ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda kara da cewa,, ma’aikatar ta kirkiro da hanya ce ta dogon zango don tabbatar da wadatar abinci a kasar nan.
Mai ba da shawara na fasaha ga Ministan Noma kan Gudanar da Ilimi da Sadarwa, Barista Richard Mark Mbaram ya bayanin cewa dabarun an yi su ne bayan an yi shawarwari da yawa a cikin kwamitin tsakanin masu ruwa da tsaki.
Mai ba da shawara na fasaha ga Ministan Noma kan Gudanar da Ilimi da Sadarwa, Barista Richard Mark Mbaram ya kara da cewa, Shugaba Buhari ya bayar da umarnin fitar da tan-tan na hatso har 70,000 iri daban-daban kuma mafi yawa na hatsi mai gina jiki an sake su daga rumbunan adana hatsi kuma an ba da su ga gwamnatocin jihohi ta hanyar Ma’aikatar Harkokin Agaji, Bala’in Bala’i da Ci gaban Jama’a, da Gudanar da Harkokin gaggawa na kasa.