Daga Abubakar Abba,
An yi nuni da cewa, ta hanyar sana’ar kiwon kifi, Gwamnatun Tarayya za ta iya wara samun kudaden shiga masu ya wa, samar da ayyukan yi musamman a tsakanin matasan kasar da su ke yin gararamba kan tituna babu aikin.
Sakataren ma’aikatar zuba hannun jari da kasuwanci na tarayya Mista Edet Akpan a yayin wata hira da manema labarai a babban birnin tarayyar Abuja inda yakara da cewa masu sana’ar za su kara samar wa da kansu kudaden shiga masu ya wa da za su kula da rayuwar da kuma ta iyalinasu.
A cewar Sakataren Mista Edet Akpan, in har an inganta ta yadda ta da ce, za ta taimaka matuka wajen samarwa da gwamnatin kasar nan da kuadaden, inda kuma ya bayyana cewa, hade dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon kifi zai bunkasa darajar kiwon kifin musamman idan su ka yi aiki tare da manufa guda wajen bunkasa kiwon kifin a Nijeriya, inda Mista Edet Akpan ya ci gaba da cewa, hade dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon kifi zai bunkasa darajar kiwon kifin musamman idan su ka yi aiki tare da manufa guda wajen bunkasa kiwon kifin a Nijeriya.
Sakataren ma’aikatar zuba hannun jari da kasuwanci na tarayya Mista Edet Akpan ya ci gba da cewa, kaddamar da jami’an yana daya daga cikin wani mataki na gwamnatin tarayya wajen tallafawa manoma da masu ruwa da tsaki wajen bunkasa ayyukansu, inda ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da jami’an gudanarwa na kungiyar kifi ta kasa NFAN ne domin t ana da yakinan hakan zai kara samarwar da kasar nan da kudaden shiga masu yawan gaske.
Sakataren ma’aikatar zuba hannun jari da kasuwanci na tarayya Edet Akpan ne ya kaddamar da jami’an a babban birnin tarayyar Abuja, inda ya kara da cewa, kaddamarwar wani mataki na samar da wani sashe da zai rika kula da kiwon kifi a Nijeriya domin cimma bukatar neman kifin da ake da shi a kasar nan.
Edet Akpan ya ci gba da cewa, kaddamar da jami’an ya na daya daga cikin wani mataki na gwamnatin tarayya wajen tallafawa manoma da masu ruwa da tsaki wajen bunkasa ayyukansu.
Ya kara da cewa, hade dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon kifi zai bunkasa darajar kiwon kifin musamman idan su ka yi aiki tare da manufa guda wajen bunkasa kiwon kifin a Nijeriya.
A wani labarin kuwa, Nijeriya na ci gaba da farfado wa daga matsalolin da ta shiga saboda irin kyawawan sakamakon da ke fitowa a musamman fanin ayyukan noma.
Wannan furucin ya fito ne daga bakin Kakakin shugaban kasa Garba Shehu, inda ya ci gaba da cewa, an samu nasarar hakan ne saboda kokarin da gwanmati ta yi wajen bunkasa aiyukan noma musamman noman shinkafa da kuma rufe iyakokin Nijeriya na kan tudu da gwamnatin tarayya ta sanya ayi.
Ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ci gaba da cewa, shekarar 2014 Nijeriya ta shigo da tan miliyan 1.2 na shinkafa amma a shekarar 2015 tan tan 58,000 kawai aka shiga da shi.
Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya ce gwamnati na goyan bayan kokarin da ma’aikatar noma ke yi na bunkasa harkar noma a sauran jihohin kasar nan.
Garba Shehu yace gwamnati za ta tallafa wa kamfanonin da ke sarrafa shikafa kamar su kamfanonin BUA dake jihar Jigawa, Dangote dake jihar Kano, OLAM dake jihar Nasarawa, WACOTT dake jihar Kebbi, da kungiyar wasu ‘yan kasuwar da tsohon gwamnan jihar Anambra ya ke shugabanta.