Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Cibiyoyin Kirkire-kirkire A Duk Yankunan Nijeriya

Daga Sulaiman Ibrahim,

Dakta Ogbonnaya Onu, Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire ya ce ma’aikatar sa za ta kafa cibiyoyin fasaha da kirkire-kirkire a shiyyoyi shida na kasar nan.

Onu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wurin taron Maulidin na 87 don karrama Cif Gabriel Igbinedion a ranar Litinin a Jami’ar Igbinedion Okada, Benin.

Ya ce cibiyoyin za su tattaro masana, cibiyoyin bincike da masana’antu don yin aiki tare a shiyyoyin don inganta kimiyya da fasaha.

Onu ya ce ma’aikatar tana aiki ba tare da gajiyawa ba don tabbatar da amfani da sabbin fasahohin kimiyya a cikin kasar.

Ministan ya nuna damuwar sa kan yadda jami’o’in Nijeriya, masana’antu da cibiyoyin bincike ba su yin aiki tare don amfanin kowa.

Exit mobile version