Umar A Hunkuyi" />

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Sabbin Kamfanonin Casar Shinkafa Guda 10

Babban daraktan bankin manoma, Alhaji Kabiru Adamu, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta amince da sake gina wasu sabbin kamfanonin Casar Shinkafa har guda 10 a sassan kasar nan, a matsayin daya daga cikin dubarunta na inganta harkar noma a kasar nan.

Alhaji Kabiru Adamu, ya fadi hakan ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki da kuma shugabannin kungiyoyin manoman da suka fito daga kananan hukumomi 44 na Jihar Kano, wanda sabuwar hukumar noman zamani da samar da abinci ta, Gezawa market commodity edchange, ta shirya a Kano.

A cewar shi, gwamnatin tarayya ta cire kudin ruwa a sashen ayyukan da suka shafi na noma wanda hakan kuma yana ta haifar da da mai ido, ya kara da cewa, shirin na kafa masanaíantar casan shinkafar a Jihohi daban-daban na kasar nan yana daya daga cikin mataki na gaba da aka dauka. Ya kara da cewa, A Jihar Kebbi kadai, a karkashin shirin nan na, anchor borrower, gwamnatin tarayya ta zuba jarin Naira bilyan 60 daga shekarar 2015 zuwa yanzun.

A Jihar Kebbi, a yanzun haka akwai kananan masanaíantun casar shinkafar wadanda suke da akalla jarin Naira bilyan biyu. Hakan yana nuna yanda dukiya ta kankama ne a Jihar ta Kebbi,î in ji shi. Tun da farko a na shi jawabin, daya daga cikin shugabannin cibiyar, Mista Bimfa Binchang, ya bayyana cewa, an shirya taron ne domin wayar da kan manoma a kan hanyoyi masu yawa na yin kasuwanci a kasuwanni, sannan kuma a ilmantar da manoman yanda za su ci gajiyar tallafin da gwamnati ke bayarwa.

Ya kara da cewa, cibiyar wacce ta masu zuba jari ce daban-daban an kafa ta ne domin ta bude hanyoyin noma na kasar nan. Ya kuma karfafa cewa, za kuma ta taimaka wajen kawar da matsalar nan ta dillalai a harkokin kasuwancin na noma, wanda yake babban barazana ne a hanyoyin cin riban da manoman suke bi.

 

Exit mobile version