Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Biliyan 600 Don Tallafa Wa Manonan Kasar Nan

Published

on

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Ministan aikin gona Alhaji Muhammad Sabo Nanono ya kaddamar da shirin bayar da bashi mara ruwa na naira biliyan 600 ga manonan kasar a garin Funtuwa dake jihar Katsina.

Ministan aikin gona ya cigaba da cewar Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Alhaji Muhammadu Buhari ta samar da wannan makudan kudaden don tallafa wa manoman domin rage masu radadin da cutar korona ta haddasa a kasar nan, Alhaji Sabo Nanono wanda yazo da shuwagabannin kwamitin aikin gona na majalisun dokoki ta kasa guda biyu na majilisar dattawa Sanata Abdullahi Adamu daga jihar Nasarawa wanda yake shi ne shugaban kwamitin aikin gona a majilisar dattawa da Alhaji Muntari Dandutse shugaban Kwamitin aikin gona a majilisar wakilai ta kasa, ministan ya cigaba da bayyana amfanin wannan shirin na samar ma matasan kasar nan ayyukan yi ta hanyar bunkasa noma kamar noman Masara, Auduga da waken soya ya ce abinda yasa aka zo Funtuwa don kaddamar da shirin kowa yasan yankin Funtuwa wajen noma a kasar nan saboda suna da kasar noma komai aka shuka a yankin yana albarka ya ce, jihar Katsina na da sama da mutum 150,000 wadanda suka yi rijista don samin wannan bashin yaci gaba da cewa shugaban kasa a ko da yaushe yana fadin cewar Nijeriya za ta noma abinda za ta ci kuma ta ciyar, babu wata Gwamnati da aka taba yi wadda ta maida hankalin ta wajen bunkasa noma a kasar nan babu shakka gwamantin Alhaji Muhammadu Buhari ta bayar da gagarumin gudunmuwa wajen bayar da rance ga manya da kananan kungiyoyin manoma.

Alhaji Sabo Nanono ya ce, a shekara mai zuwa Gwamnatin tarayya za ta samar da na’urorin noma na zamani a kowacce karamar hukuma dake kasar nan don amfanin manoman mu kuma gwamnatin tarayya za ta samar da guraben ayyukan yi ga matasan kasar nan har na mutum miliyan 10. Kowacce shekara ma’aikatar aikin gona ta tarayya za ta samar wa matasan guraben aiki na sama da mutun miliyan 5.

A nasu jawaban daban daban Shugaban kwamitin aikin gona a Majalisar Dattawa Sanata Abdullahi Adamu ya ce, a kwamitin shi da majalisar dattawa sun yaba wa Shugaban kasa wajen kokarin shi na inganta noma a kasar nan ta yadda ya jajirce wajen noman shinkafa da sauran noman kayan abinci da na saidawa a kasar nan yace yana kira ga wanda za su amfana da wannan bashi su daure suyi noma kuma zai samar da aiyukan yi ga dukkan al’ummar kasar.

Shugaban kwamitin aikin gona a majilisar wakilai ta kasa Alhaji Muntari Dandutse ya yaba ma Ministan aikin gona Alhaji Muhammadu Sabo Nanono da Sanata Abdullahi Adamu yadda aka kaddamar da wannan shirin a mahaifar shi Funtuwa da kuma jihar shi yace wannan shiri na gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Alhaji Muhammadu Buhari abin a yaba ne kuma Gwamnatin da gaske take wajen bunkasa noma kuma yace mutane da yawa suka yi rijista daga Funtuwa da Dandume don amfani da wannan sabon shirin tallafama manoman kasarnan.
Advertisement

labarai