Daga Bello Hamza
Ministan Bunƙasa Ma’addanai Dakta Kayode Fayemi ya bayyana cewa Nijeriya ta shirya kasha Naira Biliyan 42 a baɗi domin bincike da janyo masu zuba jari a ɓangare Ma’addanai domin rage dogaro da albarkatun man fetur da a ke yi a Ƙasar nan.
“da yake yanzu muka fara wannan tsari, za mu samar da kuɗin da zai ƙunshi bayanan wurare da irin albarkatun da muke da shi a sassan ƙasar nan domin anfanin masu zuba jari na ciki da ƙasashen waje” in ji shi a tattaunawar da ya yi da Wakilinmu a Abuja.
Ya ce Shugaba Buhari, ya ce gwamnatinsa ta samar da tallafi ga masu zuba jari domin haƙo ma’addanai irin su Gwal da Bitumen da Iron da Barite da Limestone da Lead da kuma zinc, gwamnati na fatan fatan samun Naira Biliya 60 na jari da ga kamfanoni masu zaman kan su.
Ministan ya kuma ayyyana cewa, “gwamnati za ta ɗauke wa sabbin ma su zuba jari a fannin ma’addanai biya haraji na tsawon shekara 5 da haraji a kan injinan da za su shigo da su da kuma lasisin izinin haƙan ma’addanai na tsawon shekara 25 domin ƙarfafa musu gwiwa a harkokin buƙasa haƙar ma’addanai a ƙasar nan”
A na ta jawabin, Babbar Sakatariya a Hukumar Bukƙasa Ma’addanai ta Ƙasa (Solid Minerals Deɓelopment Fund) Hajiya Fatima Shinkafi ta ce, gwamnati za ta bada tallafin Dala Miliyan 600 da za a yi amfani da su wajen samar da kayan aikin haƙo ma’addanai da tattara bayanai domin bunƙasa da kuma samun sauƙin haƙo ma’addanai a ƙasar nan”
“a shekarun baya ƙasar nan ba ta kulawar da ya kamata ba ga harkar haƙo ma’addanai, amma wannan gwamnati za ta canza wannan lamari domin samun ci gaban tattalin arziƙin ƙasar nan” in ji ta.
Bayani sun nuna cewa ƙasar nan na da ma’addanai fiye da 44 da za a iya fitarwa ƙasashen waje domin samun kuɗaɗe, amma a halin yanzu ɗan kaɗan ne ake haƙowa kuma ba da kayan aiki na zamani ba.