Gwamnatin Tarayya Za Ta Sasanta Da Kamfanin Twitter

Tiwita

Shugaban Kasa Buhari ya nada kwamitin da zai tattauna da kamfanin sadarwa na Twitter kan dakatar da shafin a Nijeriya. Sanarwar da Segun Adeyemi hadimin shugaban kasa kan harkokin watsa labarai ta ce an nada kwamitin ne bayan kamfanin Twitter ya rubutawa gwamnatin Nijeriya yana neman sansanci.

Kwamitin ya kunshi ministan shari’a Abubakar Malami da ministan sadarwa Isa Pantami da ministan harakokin waje Geoffery Onyeama da ministan kwadago Chris Ngige da kuma sauran wakilan hukumomin gwamnati.

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da amfani da Twitter ne bayan goge daya daga cikin sakwannin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yake yin gargaɗi ga masu fafutikar Biyafra.

Exit mobile version