Idris Aliyu Daudawa" />

Gwamnatin Tarayya Za Ta Taimaka Wa Masu Cutar Lassa

Gwamnatin tarayya zata bullo da wani sabon tsari wanda zata taimaka ma wadanda suke fama da cutar kansa, wajen samar da kuadade, shugaban Hukumar hana yaduar cututtuka da kuma maganin su ta kasa (NCDC) Dokta Chikwe Ihekweazu shine wanda ya bayyana hakan.

Ihekweazu ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya. a Abuja.

Ya bayyana dalilan da suka sa bullo da ita gidauniyar saboda, a tabbatar da ana yin amfani da su kuadaden ta yadda ba za su kasance wata matsala ba ga wadanda suke famada cutar wajen neman magani.

Ya ci gaba da bayanin cewar “ Mu na yin kokarin samar da kudade saboda tallafawa masu fama da cutar Lassa, wadda gwamnatin tarayya ce zata dauki nauyin, saboda abin zai maye magunguna ga wadanda aka tabbatar da sun kamu da cutar.

“ Ita hanya ce wadda za a iya kulkawa da kudin, maganar da akae yi kuma da alamar cewar dukkan al’amarin zai iya shafar sauran gwamnatocin.

“Babbar manufar ita ce cewar ita maganar da sai an biya kada ta kasance wata hanya wadda zata iya hana wasu marasa lkafiya wadanda kuma suke dauke da cutar samun magungunan da za su yin amfani da su wajen kawar da cutar Lassa.

Kamar dai yadda ya kara jaddada cewar gwamnatin tarayya ta fara yin wani kokari ta hanyar Hukumar NCDC saboda a yawan kudaden da suke kashewa kafin ita gidauniyar kula da lafiyar ta fara yin aiki.

Shugaban na NCDC ya bayyana cewar  “ Mu daga matakin mu na gwamnatin tarayya zamu tabbatar da cewar, su yawancin kudaden muhimman magungunan na cutar Lassa an shigar da su cikin tallafin na gwamnati. Wannan haka ne abin zai kasance saboda kuwa idan an kwantar da mara lafiya a asibiti da akwai wasu kudaden da zai biya.

“Abin da zamu yi ko kuma muka fara yi da asibitocin koyarwa shine na tabbatar da an rage yawan kudaden da su marasa lafiyar suke biya, wadanda ba za su fi karfin wanda baya da lafiyar ba.

“Ta wani bangaren kuma mun kula da cewar su wadanda basu da lafiya kyauta, ba tare da biyan wasu kudade ba, ta wani bangaren kuma akwai wadanda suke biya.

“A binda da muke son tabbatar wa shine a wuraren da ake kulawa da su marasa lafiyar, shine babu wani maras lafiyar da aka kora, saboda ya gaza ko kuma ta gaza biyan kudaden maganin, ko kuma an tare su marasa lafiya saboda sun gaza ko kuma kasa biyan kudaden maganin.

“Don haka daga karshe shine duk yadda ta kasance muna tabbatar da su wadanda basu da lafiya an samu basu magungunan da suka kamata”.

Ihekweazu ya yi kira da al’ummar Nijeriya su dauki duk wasu hanyoyin da suka dace, wadanda suka hada da hanyoyin hana yaduwar ita cutar, wato kamar wurin da aka ajiye kayayyakin abinci, da kuma tsaftace muhalli saboda yin hakan yana hana su abubuwan da suke samar da kwayoyin cutar samun wurin da za su samu yaduwa cikin sauki.

Ya kara jaddada cewar: “ Ba sai mutum ya kasance wani mai arziki bane zai iya kulawa da muhallin shi ba, don haka shi babban al’amarin shine a aika ma su ‘yan Nijeriya sakonni, ta harsuna masu yawa, wadannan abubuwan sune ake bukata saboda maganin hana yaduwar ita cutar.

“Ita hanyar hana yadiuwar ita cutar mai sauki ce fiye da maganin ita cutar, wannan ba karamin aiki bane wajen gwamnatin tarayya.

“Duk da yake dai yawan kudaden da ake kashewa wajen maganin zazzabin Lassa suna yawa matuka, mun yi wani babban al’amari dangane da kudaden da za a iya kashewa, saboda sai da muka tabbatar da cewar su magungunan da suka fii muhimmanci, a cutar Lassa an hada da su.

“Maganin Ribalbrin yana da matukar tsada amma kuma duk da hakan muna tabbatar da cewar, duk wanda aka samu ya kamu da ita cutar zazzabin Lassa ya samu maganin kyauta, amma dai koma ta ya ya ne , shi duk wanda ma ya kamau da cutar Lassa yadda zai sayi maganin abin yana kasancewa ne da sauki wajen maganin ta.

“Don haka muna kara karfafa wa masu rashin lafiya kwarin gwiwa cewar duk kua da yake suna da kudaden sayen maganin, ko nawa suke dasu, maganar samun sauki kuma wannan kuma bamu da wani tabbacin da za mu basu, dangane da yadda abin zai iya kasancewa daga karshe.

“Ina fada maku maganar gaskiya dangane da samun maganin cutar zazzabin Lassa shine, wajen kulawa da hanyoyin warkewar shi ciwon, bai wuce bin hanyar da zata hana kamuwa da ita cutar zazzabin na Lassa, ko kuma kamar dai yadda wasu mutane kan ce rigakafi yafi magani wannan tun farko ma ke nan kamar dai yadda ya kara bayyanawa daga karshe.”

Exit mobile version