Gwamnatin Tarayya Za Ta Tura Sojoji Binuwai

Majiya mai tushe daga Hukumomin Nijeriya, ta bayyanawa Jaridar LEADERSHIP A Yau cewa, Gwamnatin Tarayya ta kammala cimma matsayar yin amfani da sojoji wurin kawo karshen rikicin da kashe-kashen da ya ki ci ya ki cinyewa a Jihar Binuwai.

Majiyar tamu ta bayyana cewa an cimma wannan matsayar ne sakamakon fahimtar da aka yi na cewa wannan rikici aikin wasu mabarnata ne wadanda ke fakewa da rikicin makiyaya da manoma. Majiyar tamu ta ci gaba da cewa, wannan na daga cikin aikin da kwamitin da aka kafa na gwamoni tara makonni biyu da suka gabata.

Idan ba a manta ba, a ranar Alhamis din makon da ya gabata, Gwamnan Jihar Kano, Dakta Ganduje, wanda daya ne daga cikin membobin kwamitin ya yi wa manema labarai karin haske dangane da matsayar da suka cimma da irin shirin da suka yi na ba shugaban kasa goyon baya domin kawo karshen wannan rikici.

Kwamitin wanda aka kafa ya kumshi, Gwamnan Jihar Zamfara, Gwamnan Kaduna, Gwamnan Adamawa, Gwamnan Binuwai, Gwamnan Taraba, Gwamnan Edo, Gwamnan Filato, Gwamnan Ebonyi da kuma Gwamnan Oyo. An kaddamar da kwamitin ne a makon da ya gabata tare da yin zama na musamman da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Sai dai a jiya, majiyarmu daga hukuma ta shaida mana cewa, Sojojin Nijeriya na zaune cikin shirin ko-ta-kwana domin daukar matakan tabbatar da tsaro a Jihar Binuwai.

Sannan kuma an shawarci bangarorin tsaro, wadanda suka hada da soja da ‘yan sanda akan su kara daukar ma’aikata domin tabbatar da tsaro a fadin tarayyar Nijeriya, musamman wuraren da ake fama da matsalolin tsaro.

Exit mobile version