Idris Aliyu Daudawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KASUWANCI

Gwamnatin Tarraya Ta Kebe Biliyan N2.6 Don Aikin Tashar Mambilla A 2020

by Idris Aliyu Daudawa
October 25, 2019
in KASUWANCI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Sama da shekaru arba’in da suka shude kenan da bada kwangilar amma har yau shiru ake ji kamar yadda binciken da jaridar Daily Trust ya nuna hakan. Kwangilar wutar lantarkin da ke Garin Mambilla a jihar Taraba Jaridar ta bayyana cewa an fara bada kwangilar wannan aiki ne a 1973. A 2007 aka gwamnatin Obasanjo ta sake tado da maganar wanda shi kuma Marigayi Umaru Yar’adua ya soke kwangilar.

Bugu da kari, bayan daukar dogon lokaci, hukumar BPP ta kakakkabe takardun wannan aiki inda aka sa ran kamalla aikin a 2012. Bayan gama wannan shiri ne kwatsam sai aka maga gwamnati a kotu. Bayan wannan rikici, gwamnatin tarayya ta ci damar kammala aikin da zai samar da megawatt 3050 a shekarar 2015.

samndaads

Kamfanin EDIM na kasar Sin aka sa rai zai bada 75 bisa dari na kudin kwangilar, inda kuma kudin wannan aiki da kamfanin CGGC da Sinohydro Corporation za su yi ya karu a mulkin nan, daga Dala biliyan 3.2 zuwa Dala biliyan 5.972 wanda a kudin kasa ya haura naia tiriliyan biyu.

Har ila yau, a shekarar 2017 hukumar BPP ta ba ma’aikatar wuta sabon satifiket na samun damar fara wannan aiki da nufin cewa gwamnatin tarayya za ta nemo inda za a samu tiriliyoyin kudin da za a yi aikin, inda gwamnatin za ta bada kashi 15 a cikin dari na kudin aikin ne yayin da kamfanonin da za su dauki nauyi za su bada kaso mafi tsoka.

Za a kashe miliyan 600 ne wajen duba Mazauna Garin na Mambilla da aikin zai shafa da tsare-tsare da duba aikin da kuma aikin da kwamitin gwamnatin tarayya da jihar Taraba za su yi. Kauyuka 10000 za a tada idan aka fara wannan aikin ,unda kuma aka ba kowa kudin sallama domin su nemi wani matsugunin.
A cewar binciken, babu wasu ‘yan kwangila da su ka iso yankunan kuma Idan aka kammala wannan aiki kasar nan, za ta samu karin sama da megawatt 3000 na lantarki, inda a yanzu haka dai abin da tashar Shiroro Kainji da Jebba su ke badawa bai wuce megawatt 2000 ba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Buhari Ya Umarci NIPSS Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Kiwon Lafiya

Next Post

’Yan Nijeriya Sun Fara Sayen Shinkafar Waje A Rahusa – Hadimar Buhari

RelatedPosts

Sugar

Alakar Dake Tsakanin Sukari Ca Ciwon Suga

by Idris Aliyu Daudawa
3 weeks ago
0

Da yawa a yankin kasashen nahiyar Afirka ana ganin sukari...

A Na Cigaba Da Zaman Doya Da Man Ja Tsakanin Majalisa Da Shugaba Trump

Ba Da Mugun Nufi Shugaba Buhari Ya Garkame Iyakoki Ba – Ministar Kudi

by Idris Aliyu Daudawa
1 year ago
0

Ministar kudi da tsaretsare, Uwargida Zainab Ahmed Shamsuna, ta sanar...

Farfado Da Noman Auduga: Buhari Ya Cancanci Jinjina – Alhaji Sufyanu

Noman Auduga: Manoma 94,000 Suka Samu Tallafi A Kano Da Jigawa

by Idris Aliyu Daudawa
1 year ago
0

Sama da manoma dubu 94 da mafi yawancinsu matasa ne...

Next Post
’Yan Nijeriya Sun Fara Sayen Shinkafar Waje A Rahusa – Hadimar Buhari

’Yan Nijeriya Sun Fara Sayen Shinkafar Waje A Rahusa – Hadimar Buhari

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version