Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Gwamnatin Yankin Hongkong Ya Yi Maraba Da Dokar Tsaron Yankin

Published

on

Kantonmar yankin Hongkong Carrie Lam, ta ba da wata sanarwa game da dokar tsaron yankin musamman na Hongkong, wadda zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ya zartas a yau Talata.

A cikin sanarwar, jami’ar ta nuna cewa, kiyaye tsaron kasar nauyi ne dake wuyan yankin Hongkong, kuma gwamnatin yankin na maraba da wannan doka da kwamitin ya zartas a yau.
Ban da wannan kuma, ta ce gwamnatinta za ta kafa kwamitin kiyaye tsaron kasar, karkashin shugabancinta, bisa tanade-tanaden wannan doka ba tare da bata lokaci ba.
A hannu guda kuma, hukumar ’yan sanda, da sashin doka da shari’a, za su kafa hukuma ta musamman, don aiwatar da ayoyin dake kunshe cikin wannan doka.
A yau Talata ne majalissar wakilan jama’ar Sin, ta jefa kuri’ar amincewa da dokar tsaron kasa da aka samar, domin tabbatar da tsaro a yankin musamman na Hong Kong.
Kaza lika zaunannen kwamitin kolin ya amince da sanya dokar ciki sashe na III na dokokin yau da kullum da ake amfani da su a yankin na Hong Kong.
Ban da haka, wasu manyan kusoshin kasashen Afirka ta kudu da Madagascar da Iran da kuma Nepal, sun bayyana amincewarsu da yadda majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta kafa dokar tsaron kasa da ta shafi yankin Hong Kong na kasar, manufar da ta shafi tabbatar da tsaron kasa, don haka ba wani kuskure a ciki.
Solly Mapaila, shi ne mataimakin babban sakatare na biyu na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Afirka ta Kudu, ya nuna cikakken goyon bayansa kan kafuwar dokar tsaron kasa da ta shafi Hong Kong. Ya kuma ce jam’iyyarsa tana Allah wadai da munanan aikace-aikacen masu tada zaune-tsaye a yankin Hong Kong, da yunkurin balle yankin daga kasar Sin.
A nasa bangaren, shehun malami a jami’ar Toamasina ta kasar Madagascar Solofo Randrianja, ya ce kafuwar dokar tsaron kasa mai alaka da yankin Hong Kong, za ta taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki a yankin, da sanya manufar “Kasa daya amma tsarin mulki biyu” ta dore. (Masu Fassarawa: Amina Xu, Saminu Alhassan, Bello Wang)
Advertisement

labarai