Muhammad Maitela">

Gwamnatin Yobe Ta Ware Naira  Miliyan 441 Don Biyan Tsuffin Ma’aikata Hakkokinsu

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ga bayar da umurnin ware naira miliyan 441 don a biya tsuffin ma’aikata 321 a kananan hukumomin jihar 17 hakkokin su na fansho da garatuti.

Gwamnatin jihar ta bayyana hakan a takardar manema labarai mai dauke da sa hannun kwamishina a ma’aikatar yada labarai, al’adu da al’amuran yau da kullum, Malam Abdullahi Bego, inda ya ce wannan shi ne karo na 42 a jerin biyan tsuffin ma’aikatan jihar hakkokin su da gwamnatin ke yi don kyautata rayuwar su bayan sun yi ritaya.

Bego ya kara da cewa daga cikin wannan adadin tsuffin ma’aikata 321, daga kananan hukumomin jihar, mutum 94 sun rasu kuma za a bayar da hakkokin su ga magada wanda ya kai naira miliyan 152 da yan kai. Yayin da sauran naira miliyan 289 za a biya su ga tsuffin ma’aikata 227 wadanda yanzu haka su na raye.

Ya kara da cewa idan za a tuna ranar 11 ga watan da ya gabata na Maris 2020, Gwamna Buni ya bayar da umurnin ware naira miliyan 353 domin a biya tsuffin ma’aikata 253 daga kananan hukumomin jihar 17.

A karshe ya ce Gwamnan ya ba bayar da umurnin biyan tsuffin ma’aikatan hakkokin su a jihar ya na zuwa bayan aikin tantance ma’aikatan da su ka yi ritaya a daukwacin kananan hukumomin jihar, ta hanyar kwamitin da aka kafa wajen gudanar da aikin a kowane lokaci.

Exit mobile version