Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya rushe dukkan sakatarorin kananan hukumomin guda goma sha hudu tare da nada wasu sabbi.
Haka kuma gwamnan ya amince da nadin shugaban makarantar Koyon fasaha da Kwalejin ilimi na jihar.
Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai wadda ke dauke da sunan babban daraktan yada labaran gwamnan Yusuf Idris.
Gwamnan ya umarci dukkan sakatarorin kananan hukumomin da su mika dukkan kayan aikinsu ga ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu.
Sabbin sakatarorin da aka nada su ne Abubakar Bakura, karamar hukumar Bakura; Rabi’u Pamo, Anka; Abdulkadir Gora, Birnin-Magaji; Lawali Zugu, Bukkuyum; Sani Mainasara Bungudu, Rabi’u Hussaini, Gummi da Nura Musa wanda aka sa shi a Gusau.
Sauran su ne Bashir Bello, karamar hukumar Kaura-Namoda, Ahmadu Mani, Maradun, Salisu Yakubu, Maru, Abba Atiku, Shinkafi; Ibrahim Garba, Talata-Mafara; Aliyu Lawali, Tsafe da kuma Bala Dauran karamar hukumar Zurmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa, Dakta Sha’aya’u Mafara shi aka nada shugaban makarantar koyon fasaha sai kuma Muhammad Maradun aka nada shi rajistaran makarantar koyon fasaha ta Abdu Gusau da ke, Talata-Mafara.
Haka kuma Matawallen ya nada Ibrahim Gusau shugaban Kwalejin ilimi da ke Gusau.
Saboda haka gwamnan ya bukaci dukkan wadanda aka tuben da su mika bayanan tafiyar da ofishin nasu ga ofishin gwamna.