Daga Hussaini Yero,
Gwamnatin jihar Zamfara, karkashin jagorancin Gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun,tasa takalmin karfe ga Maharan da basu yarda da sulhuba a fadin Jihar ta Zamfara .
Kwamishina ‘Yan Sandan Jihar Zamfara,CP Abutu Yaro ne ya bayyana haka jinkadan bayan kammala taron Sarakuna da Malamai da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a gidan gwamnati da ke Gusau.
Kwamishina Abutu Yaro,ya bayyana cewe,’Samakon taron akan tsaro da Sarakuna da Malamai Addini da Shugabannin tsaro na Jihar karkashin jagorancin Gwamna Bello Muhammed Matawallen Maradun ,kowa ya aminta da cigaba da sasanci ga masu tayar da kayar baya masu kai hare haren a fadin Jihar dan samu nasara dawamamen zaman lafiya, inji Kwamishina Abutu.
“Abutu Yaro ya kuma tabbatar da cewa,duk bangaren da bai aminta da sulhu ba ,lallai zai gamu da fushin jami’an tsaro dan haka duk wanda yasan yana da hannu acin ‘ta’addancin da akeyi a wannan jiha ya gaggauta tuba masu makamai su kawo makaman su kofa a bude take, inji Kwamishinan.
Haka kazalima Sarakuna da Malaman Addini sun dau alwashin shiga lunguna da sako dan sasantawa da wadannan maharan a duk inda suke da kuma fadakar dasu illar ayyukan ta’addanci da ‘yan ta’addan keyi badare babu Rana.