Gwamnatin Zamfara Za Ta Zamanantar Da Asibitin Kwararru Na Yeriman Bakura Da Daga Darajarsa  
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Zamfara Za Ta Zamanantar Da Asibitin Kwararru Na Yeriman Bakura Da Daga Darajarsa  

byLeadership Hausa
2 years ago
zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya amince da shirin gyara, tare da sake inganta asibitin ƙwararru na Yeriman Bakura da ke Gusau domin magance ƙalubalen da ake fuskanta na samar da ingantaccen kiwon lafiya a Jihar Zamfara.

Gwamnan ya amince da aikin gyaran asibitin ƙwararrun ne a ranar Litinin a taron Majalisar Zartarwa karo na sha tara a gidan gwamnati da ke Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa za a fara aikin gyaran ne nan take, kuma ana sa ran gyaran zai mayar da asibitin zuwa babbar cibiyar lafiya ta zamani kuma mai isassun kayan aiki irin na zamani.

A cewar sanarwar, an yanke wannan shawarar ne a daidai lokacin da aka ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren kiwon lafiya na Zamfara.

  • Sojoji Sun Hallaka Kasurgumin Dan Bindiga, Kachalla Damina Da Yaransa

Ya ce, “A jiya lokacin da Gwamna Lawal ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa, ya amince da yadda za a yi gaggawar gyara asibitin ƙwararru na Yeriman Bakura.

“Asibitin ƙwararru na jihar ya daɗe a lalace kuma ba shi da isassun kayan aikin kiwon lafiya. Hakan ke tilasta majiyyata yin tattaki zuwa Sakkwato ko Kaduna domin samun wankin ƙoda da sauran gwaje-gwajen lafiya.

“Alhaji Mustapha Falaki, Shugaban Cibiyar Kiwon Lafiya ta Minjirya, ya gabatar wa majalisar koke kan halin da asibitin ƙwararrun ke ciki a halin yanzu da kuma matakan da za a ɗauka na sake fasalin cibiyar.

“A cikin shirin gyaran asibitin, za a gina sabbin gine-gine da wuraren kiwon lafiya, za a samar da na’urorin kiwon lafiya, sannan a horar da masu amfani da na’urorin don mayar da asibitin ƙwararru ya zama wurin kiwon lafiya na zamani da ingantattun kayan aikin da za su samar da ingantacciyar kiwon lafiya ga al’ummar jihar.

A yayin taron majalisar, an tattauna batutuwa masu muhimmanci da dama. Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna shi ne manufofin kyautata jin daɗin jama’a da zamnatakewa a jihar. Wannan manufar na da nufin haɗa kan al’umma daban-daban da inganta walwala waɗanda suka dace da hangen nesan Jihar Zamfara a matsayin ɗaya daga cibiyar ci gaban al’ummar Nijeriya. Manufar ita ce tsare-tsare don taimakawa wajen jagorantar zuba jari a harkokin gwamnati da masu zaman kansu don inganta jin daɗin jama’a da zamantakewarsu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya
Labarai

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba
Labarai

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Next Post
Amurka

Fahimtar Juna Tsakanin Matasan Sin Da Amurka Zai Haskaka Makomar Dangantakar Kasashen Biyu

LABARAI MASU NASABA

…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version