Gwamnoni Sun Gaza Wajen Magance Ambaliya – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta ce akwai sakacin gwamnatocin jihohi game da dakile ambaliyar ruwa tare da sakacin tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Ta bayyana hakan ne a ranar Laraba a cikin wani shirin amsa tambayoyin daban daban da Hukumar Kula da Ayyukkan Tsarin Tsirrai ta Najeriya (NIHSA) da Hukumar kula da sararin samaniya (NiMET) ta kasa tayi.
Kungiyoyin sun yi magana a wani shirin horarwa kan amfani da bayanan tauraron dan adam don yin hasashen ambaliyar.
Taron ya sami goyon baya daga kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) a karkashin shirinta na Kula da Duniya da Tsaro na Afirka (GMES & Africa) wanda Cibiyar Nazarin Ilmi da Fasaha ta Kasa (CSSTE) ta gudanar.
Darekta-janar na NIHSA, Clement Nze, ya ce dole ne gwamnatocin jihohi su taka rawa ta wajen yin amfani da bayanan da aka basu don hana masifar ambaliyar.
Ya ce NIHSA da sauran hukumomin Gwamnatin Tarayya suna cikin wani bangare na binciken da ya shafi annobar sararin samaniya, ya zama dole gwamnatocin jihohi su dau alhakin daukar matakai na kare dukiyoyi da rayukan al’umma.NAN

Exit mobile version