Bello Hamza" />

Gwamnonin Arewa Sun Yi Alkawarin Farfado Da Martabar Sardaunan Sakkwato

Gwamnonin Arewa

Shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya bayana cewa, kungiyar za ta jagoanci farfado da martabar marigayi Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya ke karbar bakoncin shugaban tsafoffafin daliban makarantar Kaduna Poly Kaduna a karkashin shugaban kungiyar ta kasa, Mr Abbas Adamu, a gidan gwamnati da ke Jos.

Lalong ya ce, Marigayi Sir Ahmadu Bello ya kasance Firayministan yankin arewa na farko kuma na karshe a tarihin yankin.

Ya kuma kara da cewa, a taron da kungiyar ta yi kwanakin baya a Kaduna tare da sarakunan gargajiya, kungiyar ta yi alkawarin tattaunawa tare da masu ruwa da tsaki don fito da hanyoyin da za a tabbatar da farfado da martabar Sardaunan musamman ayyukan da ya yi na bunkasa yankin arewa wanda ake cigaba da cin gajiyarsu a halin yanzu.

Gwamnan ya kuma ce, za a duba wurare irin su jami’ar ABU da makarantar Kaduna Poly don ganin irin matalolin da suke fuskanta tare da fito da hanyoyin tallafa musu.

 

 

Exit mobile version