Connect with us

LABARAI

Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Zulum

Published

on

kungiyar Gwamnonin Arewa ta yi tir da harin da aka kai wa Gwamna Babagana Zulum na Borno ranar Laraba, inda ta bayyana harin a matsayin ta’addanci.
Shugaban kungiyar kuma Gwamnan Filato, Simon Lalong, ne ya yi Allah wadai din cikin sakon da Daraktan watsa labaransa, Dakta Makut Macham.
Ya ce harin da aka kai wag Gwamnan a kan hanyarsa ta Baga cikin karamar hukumar Kukawa ta jihar wani aiki ne na kokarin hana shi taimaka wa raunanan al’ummar jihar.
Gwamnan ya nuna damuwarsa ganin cewa an kai wa Zulum hari ne lokacin da yake kan hanyarsa ta kai wa ‘yan gudun hijira kayan hidimar Sallah.
Lalong ya ce harin wani aiki na daga wasu baragurbin da suke kokarin hana gwamnan rage wa ‘yan gudun hijira radadin da ‘yan ta’adda suka jefasu ciki.
“Wannan harin ya nuna karara akwai masu makiya zaman lafiya da mutane da basa jin dadin rage wa jama’a wahala da Gwamnan yake.
“kungiyar Gwamnonin Arewa cikin kakkausar murya na Allah wadai da wannan harin, kuma tana goyon bayan Gwamna Zulum wanda ya nuna kwazo wajen kai wa mutane tallafi ko da yana cikin hatsari.
“Muna kira gare shi da kada ya taba tsorata yayin da yake aiki tare da jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyar al’ummar,” inji shi.
A wani labarin kuma, kungiyar Gwamnonin Arewa ta yi ta’aziyyar mutuwar dattijo kuma Shugaban kungiyar Yarbawa ta Afenifere, Ayorinde Fasanmi.
Lalong cikin sakon ta’aziyyar ya bayyana mutuwar dattijo a matsayin gagarumar rashi ga kasar Yarbawa da Nijeriya baki daya saboda gudumawar da ya bayar wajen ci gaban siyasar Nijeriya.
Ya yi ta’aziya ga iyalan Ayorinde Fasanmi, abokan siyasa da mabiyansa, inda ya yi Allah Ya gafarta masa.
Advertisement

labarai