Gwamnonin Kudu Ku Dau Darasin Siyasar Awolowo Da Abiolo Ba Barazana Ba – Sani Brothers

Sani Brothers

Alhaji Sani Yunusa Sarina wanda aka fi sani da Alhaji Sani Brothers daya daga cikin dattawa Nijeriya da ke zaune a Kano tsohon shugaban kungiyar sufiri ta Nijeriya mai fashin baki da bin al’amuran yau da kullum da yin nasiha ko jawo hankalin al’umma da hukumin da cigaba kasar mu, ya yi tsokaci kan maganar gwamnonin kudu da sauran batutuwa da suka shafi Nijeriya. Wakilinmu MUSTAPHA IBRAHIM KANO ya zanta da shi, ga yadda ta kasanceahirarsu.

Ba da dadewa ba ne Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ba Mai Martaba Sarkin Kano na 15 a Daular Fulani Sandar mulki da kuma ratsar da shi ko akwai shawara ko tsokaci, kasancewarka daya daga cikin dattawa?

To godiya ta tabata ga Allah madaukakin sarki kan wannan lamarin na Allah da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya gaji Mahafinsa kuma Gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince ga shi har ambashi sandar girma da rantsiwar kama aiki kuma Jama’ar Kano sukaba da hadin kai da goyan bayan su wannan abu ya yi kyau abun da za mu ce kawai shi ne su yi koyi da yadda mahafinsu ya yi na kyakyawar mu’amala da taka tsan-tsan adukkanin lamarin da hakuri da jama’a da kyautatawa kamar yadda ya kamata da adalci a duk wani abu da ya taso, kuma inda mahafinsu ya gaza su yi kokarin gyarawa kasancewar dan Adam dukka ajizi ne wannan shi ne abun da zance kenan da Mai Martaba Sarkin Kano da dan uwansa Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero. To indan su ka yi haka komai zai yi dai dai insha Allahu. Allah ya yi musu jagora da sauran shugabanin na Nijeriya.

A yan kwanki da suka gabata gwamnonin kudu sun yi barazanar cewa dole ne shugaban kasa sai ya fito daga kudu a zaben 2023 in Allah ya kai mu lafiya, kana da abin cewa?

Abin da zance kawai shi ne ita dimokuradiyya  ba ta amfani da wani abu na barazana sai dai yawan jama’a kuma tun da Nijeriya daya ce wannan abu ne mai sauki ba mu ce kar ‘yan kudu su nemi mulki ba amma abun da ya kamata shi ne duk maisan mulki shi ne yake fitowa ya nemi magoya baya amma babarazana ba ko tilastawa ba. Domin akwai misalai masu yawa na hakan amma ga kadan yanzu a zaban 1990 ko na jam’iyar NRC da SDP da aka yi takara tsakanin marigayi MKO Abiola da Alhaji Bashir Oathman Tofa, dan tofa dan Kano usul l!amma Abiola na SDP daga Legas ya ka da Bashir Tofa a Kano ka ga wannan darasi ne ga su wadannan gwamnoni na cewa ‘yan Arewa ba sa kyamar kowa nan kai dai ka nemi jami’an su amince maka kawai amma ba ba barazana ba. Domin dai ba bangare daya ne zai zabe ka ba. Dole kowa ya samu jama’a a ko’ina amintattu a tsakanin ma’abota addini da harshi mababanta kana da jama’a da za ta tallata maka manufa ga jama’ar warin wato sako da lungu na kudu da arewa tunda dai kasar daya ce amma ba barazana ba.

Kuma abun da na keso shi ne gwamnoni kudu su dauki darasin siyasar marigayi Chief Awolowo da Marigayi Abiola, amma ba barazana ba domin kuwa kamar yadda na gaya ma a bayanan shi ne Abiola ya yi aiki sosai har ‘yan Arewa suke son shi har ya kada dan Kano cibiyar Arewa a Kano Alhaji Bashir Tofa, wannan ya nuna ba a kyamar dan ko wane bangare daga Arewa kenan, kuma Arewa mun yadda cewa Arewa ba ta mulki sai da kudu, mu Arewa mun san haka kuma mun yarda.

Kuma Gwamnonin kudu su dau darasi na matsala da marigayi Awolowo ya samu shi ne ya yi siyasa irin ta wayo! wacce ta hana shi cimma burin siyasar sa domin shi ne wanda bai yarda da kowa ba Arewa in ya zo birni ko kauyea Arewa kamfen a jirginsa yake zuwa ba ya kwana ko ruwan gari ba ya sha na arewa yake komawa gida wanda ya kamata a ce ya na da aminai a ko ina da ya in ya je kamfen ya na da inda zai  kwana a yi a hira a ci a sha shi ne siyasa, ko da kowa irin su Malam Aminu Kano duk banbanci siyasa bai kamata ya hana Awolowo yarda da ‘yan arewa kwata-kwata ba, hakan ce kuma ta ja masa matsala a siyasar wanda kuma shi ya kamata shi ma ya zama darasi ga ‘yan siyasar kudu, musuman shugabanin su ko gwamnoni su kuma duk wanda ya dau akidar Awolowo, sai ya samu matsala da kyamar jama’ar Arewa.

Duk a wannan zaman na gwamnoni sun yi maganar ba da wa’adin hana kiwo zuwa watan 11 na 2021, me za ka ce kan wannan batu?

To Abun da zan ce dai shi ne kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ce duk dan kasa yana da ikon zuwa ko wacce jiha ya zauna ya yi walwala ga mu ‘yan arewa mun yadda da haka kuma mu na dabaka haka domin kowa tun daga Iloron har zuwa Sokoto ba wani lungu da za ka samu a ce ba wani Bayerabe ko Inyamiri yana kasuwancinsa batare da wata tsangwama ba kuma sun haka, kuma suma a kudu haka abin ya ke a gunsu ko?

Haka kuma ka da su manta cewa wannan maganar hana kiwo ta saba wa tsarin kundin milkin Nijeriya, haka yau wannan magana na hana kiwo kada su manta cewa da su ne ke cin naman dabbobin Nijeriya kuma in ka duba sun fi kowacin gajiyar wannan kiwo kuma abun mamaki shi ne ba ki ya san abun da zai fada amma bai san abun da za a ce masa ba, haka kuma idan ‘yan Arewa su ma sun ce dan kudu ya koma kudu yaya kenan?

Dole dai mu yi mu’amala da sanin ya kamata da mutunta juna ba kyamar juna ba domin idan mutun yana da tunani da basira ya rika tunani a kan ko wacce magana da irin martininda za a maida masa da ita musumman mutumin da ke ikirari shi masanin shari’a ne da dai sauransu.

Yanzu haka Gwamnatin Mahammadu Buhari ta APC ta cika shekaru shida, me za ka ce kan hakan?

To wannan magana ce domin duk wani abu za ka ga cewa akwai wani abu na yabo da na suka ko kuma abu mai amfani kuma akwai mara amfani tsarin Gwamnatin Buhari abu ne mai kyau amma matsalar ita ce wajen aiwatarwa a nan amatsalar take domin wajen bayar da kudin tallafi ko bashi ga ‘yan Nijeriya abun da ya kamata shi ne aba wadan da suka san yadda su ke da ilimin gina masana’anto a zahiri ba masu ilimi zaune a kan tebir ba ‘yan bokon cima zaune ba domin kudin da ya kama ta an ce a ba kamfanonin da suka durkurshe an yi shiri da CBN na ba biyan kashi tara mai makon sama da haka da ake yi a yanzu na kudin riba da hakan ya sa kamfanoni da yawa su farfado, matasa da dama sun samu aikin yi kuma kaya za su zama masu sauki kamar yadda ya kamata domin yanzu mu a nan Kano idan ka je Bompai za ka samu kamfanoni sama da kashe 90 acikin 100 ba sa aiki, daruruwan kamfanoninmu na Kano, ka ga da wadannan kudi da ake ba mutun daruruwa ko milliyoyin Nairori ga wanda bai san yadda ake sarrafa kudi kadan su zama masu yawa ba domin idan ka ba irin wadannan matasa da ba su taba samun irin wannan kudi kamar Milliyan 10, ko Milliyan 5 to mai hikima ne cikin su zai kashe milliyan biyar ne wajan gina gida bayan siyan  mota da dinki na kece raini, sannan ya yi tunanin sana’ar da zai yi da sauran Milliyan biyar din tunda bai san nema ba ai Buhari ya yi gaskiya da ya ce matasanmu cima zauna ne domin akwai masu tunanin da sun gama digiri sun gama wahala sai kudi kawai a huce da sauransu a rayuwarsu ta duniya to ka ga ba da kudin a gwamnatin Buhari abu ne mai kyau amma ka ga akwai gyara wajen aiwatarwa, a nan matsalar take.

Har ila yau wajibine ko shawara ga gwamnoninmu su masu samar da tsarin sarrafa dazuka mu dan yin noma na zamani da samar da aikin yi ga matasa da kuma samar da abinci ga ‘yan kasa ta hanyar sarrafa dajin mu za a samar da burtala ga makiyaya da wurin noman kaya cimaka irin su Masara, Gero, Shinkafa, Dawa, Maiwa da sauransu haka kuma ana ne za a samar da wurin noman auduga, gyada, wake da makamantansu domin samar da kudin shi ga ta hanyar noma

A karshe mene ne shawararka ko sakonka ga hukumomi da sauran al’umma?

A yi adalci kuma ba a makara ba amma duk abin da za a yi a sa masanana gaskiya ba masu takama sun yi karatu a takarda ba, a ji tsoron Allah, shi ne maganin duk wata matsalar Nijeriya. Na gode.

 

Exit mobile version