Umar A Hunkuyi" />

Gwamnonin Nijeriya Za Su Yi Wa Cutar Zazzabin Beraye Taron Dangi

Kungiyar gwamnoni ta kasa ta ce tana yin aiki tare da ma’aikatar Lafiya ta tarayya da sauran hukumomin da suka dace domin magance bullar Cutar zazzabin Lassa a cikin kasar nan, da kuma dakile duk wata barazanar cuta makamanciyar ta a cikin kasar nan.

Shugaban kungiyar gwamnonin ta kasa, Gwamna Kayode Fayemi, na Jihar Ekiti ne ya bayyana hakan ga manema labarai a bayan wani taro da kungiyar na su ta yi ranar Laraba, da dare a Abuja.

Fayemi ya bayyana cewa, kungiyar ta su ta ji bayanin halin da ake ciki a kan matsalar bullar zazzabin na Lassa da kuma cutar “coronabirus” wacce ke kashe mutane a kasar Sin, wacce kuma take ta yaduwa zuwa sauran kasashen Duniya.

“Kungiyar mu ta ji bayanin halin da ake ciki a kan zazzabin na Lassa daga kungiyar gwamnonin Arewa, a kan ayyukan lafiya da kungiyar za ta mayar da hankali a kansu a wannan shekarar ta 2020, da suka hada da kaddamar da wani taron kwanaki biyu na musamman da kungiyar ta yi a kan kula a hanyoyin kiwon lafiya a watan Nuwamba, 2019, (wanda kuma gidauniyar Dangote ce da kuma ta Bill da Melinda Gates) suka dauki nauyin sa.

“Dangane da zazzabin na Lassa, mun sami rahotannin bullar cutar a Jihohi daya ko biyu, Jihar Ondo a kudu maso yammacin kasar nan da kuma Kano a Arwwacin kasar nan.

“Ina da tabbacin dukkanin Jihohinmu suna daukan matakan kare kai tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta tarayya da kuma cibiyar kula da bakin cutuka ta kasa.

“Muna aiki tukuru domin tabbatar da cewa cutar ba ta ci gaba da yaduwa ba a halin yanzun,” in ji Fayemi.

Ya ce Gwamnonin kuma sun amince da sake duba ayyukan cibiyoyin lafiya a Jihohin kasar nan, a taron shugabannin kungiyar gwamnonin da za a yin a zango-zango, domin duba kokarin da Jihohin ke yi da kuma abin da Abuja ke yi a wajen taron tare da yin taro da shugabannin al’umma da shugabannin Addini.

Jihohin da suka sami wakilci daga Gwamnonin su a wajen taron sun hada da Jihohin, Ekiti, Osun, Ondo, Kogi, Kebbi, Filato, Yobe, Neja, Delta, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, Gombe, Borno, Oyo, Kogi, Anambra, da Enugu.

Wakilan tawagar a karkashin jagorancin Pantami sun hada da, Mataimakin shugaban hukumar sadarwa ta kasa Farfesa Umar Danbatta.

 

Exit mobile version