Umar A Hunkuyi" />

Gwamnonin PDP Biyar Na Neman Hadin Kan Buhari Kan Zaben 2019

Rahotanni sun nuna cewa wasu gwamnonin Jam’iyyar PDP biyar, biyu daga sashen kudu maso kudancin kasar nan, uku kuma daga sashen kudu maso gabashin kasar nan suna neman kulla wani alkawarin sirri da Shugaba Buhari, a kan babban zaben watan Fabrairu na shekarar 2019.

Rahotannin sun ce, gwamnonin na PDP suna neman kulla yarjejeniyar ce da Shugaba Buhari, domin su sami zarcewa a kan kujerun su.

Gwamnonin na PDP suna neman kulla yarjejeniyar ne a daidai lokacin da wasu ke ta ficewa daga Jam’iyyar, kamar yadda a baya-bayan nan ake yada cewa, tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau da na Jihar Kuros Riba, Donald Duke, sun fice daga Jam’iyyar ta PDP.

A cewar rahotannin, daya daga cikin gwamnonin ne ya fara kawo shawarar a kulla yarjejeniyar, wace ta burge sauran hudun su ma suka goyi baya.

Majiyar ta fadar Shugaban kasan cewa ta yi: “Gwamnonin biyar suna rokon shugabannin Jam’iyyar PDP ne da su taimaka masu su kulla yarjejeniyar da Shugaba Buhari, domin ya kyale su a sake zaben su, su kuma za su taimaka ma shi ya cinye zaben Jihohin su.

“Gwamnan da ke jagorantar sauran gwamnonin, wanda ya fito daga Jihohin kudu maso kudu, yana kan yin magana a yanzun haka da wasu gwamnonin APC biyu domin su gabatar da bukatar na su ga Shugaban kasan kafin su zauna da shi ido-da-ido.”

An ce jagoran gwamnonin yana ta ci gaba da matsa wa gwamnonin na APC kaimi musamman ma a lokacin da Shugaban kasan yake ziyarar sa ta kasar Sin.

Exit mobile version