Gwamnonin PDP Sun Caccaki Sojoji Kan Kisan ‘Yan Nijeriya

Kungiyar gwamnoni ta jam’iyyar PDP sun caccaki sojoji dangane da yawaitar kashe-kashe da matsalolin tsaro da su ka addabi Najeriya.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya sanya wa hannu a jiya Litinin, kungiyar sun yi Allawadai da kashe-kashen da aka yi a Taraba da jihar Abia hadi da zargin cewar sojoji sun kauce wa tsarin dokar kasa da ya samar da su na kare iyakokin kasa daga barazanar da ka iya shigowa cikin kasa.

Kungiyar ta na mai karawa da cewar zargin kisan ‘yan sanda guda uku da ake yi wa sojoji da wani farar hula guda daya a jihar Taraba da kisan wani dan kabu-kabu mai motar haya a Abia a ranar Labara da yamaci abun kaito da tir ne.

A cewar sanarwar; “Wadannan yawaitar kashe-kashe a ‘yan kwanakin nan, sun sake daukar wani babi na abun haushi na mummunar yanayi ba kawai rashin imani ko tausayi ba ne, a’a hakan ma mugunta ne kuma zalumci ne, sannan rashin kwarewa ne a samu faruwar hakan daga sojoji, ko kadan ba za mu lamunci irin wadannan munanan dabi’un a kasar nan ba,” A cewarsu.

Sun ce, da bukatar sojoji su koma asalin tsarin da ya samar da sun a kare iyakokin kasa; “Muna sake nanata cewar wadannan kashe-kashen ba sune muke so ba.

Abun takaici ne a ce sojoji za su yi watsi da tsarin mulkin kasa da ya samar da su domin kare iyakokin kasa daga wani abun illa da zai shigo cikin kasa na ta’adda,” a cewar Gwamnonin.

Exit mobile version