Daga Mustapha Ibrahim,
Taron bakin kadamar da litafin sallatin Annabi Muhammad Sallallahu a Alaihi wasallam ya yi armashi kuma Gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje da Masarautar Kano bisa jagorancin Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da sauran sarakuna daga masarautar Bichi, Rano, Karaye da Gaya da asttajiran Kano irinsu Alhaji Kabiru Sani Kwangila da ’yan siyasa irinsu shugaban karamar hukumar birnin Kano, Hon. Hafiz Alfindiki, sun yi rawar gani wajen samun gagarumar nasara a wannan biki na kadamar da litafin da Malama Hajara Muhammad Kabir ta walafa a wannan lokaci.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban Kwamitin aiwatar da taron kaddamar da littafin, Malam Nuhu Gudaji, a zantawarsu da wakilinmu ta wayar tarho bayan kammala taron, wanda aka yi a ranar Asabar da ta gabata a harabar Masarautar Kano dake Kofar Kudu a karamar hukumar birnin Kano.
Har ila yau ya ce, yadda Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da littafin akan kudi Naira Miliyan guda bisa wakilcin Sakataren Gwamnati kuma Wazirin Masarautar Gaya, Alhaji Usman Alhaji, abun a yaba ne ganin yadda Gwamnatin Kano ta ba wa abun mahimanci.
“Duk wannan sun cancanci yabo da sauran al`uma da suka fanshi litafin akan farashi daban-daban da ma sauran al’umma da suka bada gudunmawa wajen samun nasarar bikin kaddamar da littafin na Malama Hajara Muhammad Kabir.”
A nata takaitacen jawabin godiya da ta yi Malama Hajara ta bayyana makasudin wannan littafi, inda ta ce domin zaburar da matasa da yara maza da mata sanin muhimmancin salatin Annabi Alhis salam da kuma riko da shi, domin samun tsira a duniya da lahira inda kuma ta yi godiya ga Gwamnan Jihar Kano da daukacin shugabanni da sarakuna da sauran al’umma bisa gagarumar gudunmawa da hadin kai da al’umma ta bayar a wannan muhimmin taro.