Gwarzonmu Na Mako: Kammala Tattaunawa Da Sanata El-Jibril Doguwa

Ya makomar su wadanda ka koma APC din da su tunda ba wata yarjejeniya?

Makomarsu Alhamdlillahi kada ki manta shi tsari a harkar siyasa a hankula yake zuwa. Misali ni ba g a shi an ba ni mukami ba tare da na sani ko na nema ba. Speaker ya ba ni special adbisor yanzu da na ce me za a ba ni watakil ma da a Kano zan dan rabe watakil na ce a ba ni dan mu’abban ofishin gwamna ko a ban i Danmakwayon ofishin gwamna amma ina zaune da yake ina da da abokin tafiya Honourable Alasan Ado Doguwa me kishin Kano ya ga wannan mukamin ya cancanta da ni ya nemi alfarma gun Mr Speaker kuma aka amince.

 

Yanzu ka koma gwamnatin tarayya, ka bar siyasar jiha?

Yanzu saboda da Allah ni duk mukaman da na rike a Kano a ce har yanzu ana kokawar neman mukami da ni a Kano? Ba wai ina nufin na fi karfin duk mukamin da za a ba ni ba ne a Kano ban fi karfin wannan ba amma kuma ba za a ganni ina kokawar nema ba. An kai wani kadami da ba zan yi kokawa da yara ba.

 

Haka za ku bar abin sasakai, ba wani tsari a siyasar kasar?

Ai mu ma ba ma jin dadi saboda ma rashin jin dadin Muna nan muna wani tsari na kafa wata tafiya me suna Kano Peace Makers wato ma’ana dattawa ne duk inda muka ji abu ban a dadi ba za mu je mu tunkari mutum mu ce wannan abin ba zai yi wa Kano dadi ba. Wato fa mun sha wuya. Ina tuna lokacin da na yi bautar kasa wato Kano tana da kima ana girmama duk wanda ya ce daga Kano yake za ki ga yanda ake kimanmu shi da ba mu wata daraja ta musamman a lokacin nan duk kabilun nan mun fi su martaba. Amma yanzu mun banzatar da darajarmu da girman da Allah ya ba mu. Dole sai an sami wadanda za su din ga fadawa mutane Gaskiya Kai hatta baya – bayan nan zamanin Abacha ki bibiyi yadda ake ganin girmanmu da Allah ya ba mu amma mu mutanen Kano yanzu muna wasa da kyautar da Allah y aba mu.

 

Ya tsarin wannan sabon ofishin naka ya ke?

To tunda aka ce mataimaki na musamman to speaker na iya dora ma nauyi ta kowanne bangare musamman ma kuma ni da nake da sani akan abubuwa misali abin da ya shafi majalisa wanda na yi sanata na shekara hudu a wannan camber na rike kwamiti na zauna a airforce na mataimakin shugaba da kwamiti-kwamiti na abin da ya shafi water resources da na works duk ina da haske a wajen in kuma ya ce ga wannan so naka ka zauna a nan kawai ga aikinka zan yi saboda na riga na karbi appointment din.

 

Ya ka ke kallon adawa a baya da a yanzu kuma?

Ai ita kanta adawa a cikin jam’iyya ado ce ga mai mulki tana kara sa wa mulkinsa ya yi kyau da ya saki linzaminsa da an je an yi masa wata kalma ta adawa za a ga ya fara jan linzami sai ya dawo kan sirdi. Lokacin da nake shugabancin jam’iyya na yi adawa duk wanda yake Kano ya sanni akan maganar adawa amma adawa ba ta zage-zage ba irin wadda ake shiga cikin Radiyo ana ambatar sunaye na masu mutunci da kima kana bata su. Adawa ta manufa nake. Misali Malam Ibrahim Shekarau lokacin yana gwamna a jam’iyyar ANPP ni kuma ina shugaban jam’iyyar PDP a jahar Kano mun yi adawa, duk aikin da ya yi in muka ga kamar zai yi gwaninta sai mu gindaya wani itace na adawa muna sane amma ba cin mutunci. Misali akwai wata hanya da yake yi wadda ya sa wuta a kan titin daga dangi har tukuntawa mun san hanyar nan za ta taimaki al’umma a lokacin sai na ga ya kawai malam Ibrahim Shekarau muna zaune ya za ya dauke credict din mu ba mu yi ba. Don haka sai na shiga radiyo na ce mu fa muna son malam Ibrahim Shekarau ka zo ka fada mana don mun san gwamnatin tarayya ta shirya za ta dau manyan garuruwa guda biyar daga ciki akwai Kano da Lagos da Fatakwal da Inugu akwai Abuja an ce za a mayar da su Mega City a sa fitilu ko’ina su koma kamar kowanne gari a duniya don haka muke tambaya wannan aikin da ya yi yana daga ciki ne? Ai kuwa daga ji ya ce Ya salam! Ai wannan aiki na gwamnatin jaha ne kin ga wannan adawa ce mai ma’ana. A irin wannan adawar ta batanci ni anan ake batawa da ni. Sam ba ma na goyon bayanta.

 

Wanne kira za ka yi wa APC kada su fada irin Mmatsalolin da PDP su ka shiga a baya na rashin alkibla?

To, za ka yi kira amma kin san ji ba dole ba ne watakila wasu daga cikin shugabanni ya kamata su san wannan babban abin da yake muhimmi a gare su shi ne su tsaya su shirya wa matasa, hankalinsu ya tashi daga yin ba dai-dai ba ya zamana hankalinsu ya dawo kan neman na kansu. In kika duba Kamfen da wajen taro in da za ki hau mumbarin taron da za ki iya kirgawa to za ki iya kirga wadanda ke da hula a kansu. Kin kuwa san hula a kai alama ce ta dattijantaka kin ga duk matasa ne. Ashe kuwa idan ba a yi musu kyakkyawan tsari ba to za a fada rikici. Alhamdulillahi Allah ya ba mu gwamna a karkashin jam’iyyar APC Dr Abdullahi Umar Ganduje Amma saboda yawan mutane da yawan matasa sai al’umma ta hada kai kuma an aba shi shawara kuma sai al’uma da yi yunkuri ta taimaka wa gwamnatin.

 

Ta ya ya za a taimaki gwamnati?

Kwarai kuwa yanzu mu muna nan muna wani shiri za mu yi Voluntry teachers association kungiya ce da za mu san su wa ye masu digiri a bangaren education ba su da aiki sannan za a tafi kasa-kasa a nemo wadanda suke harkar kiwon lafiya ba su da aiki za mu je wajen gwamnatin mu fada mata mun yarda za a yi aiki boluntary tunda ba za a iya daukar ma’aikata ba amma mun san duk karamar hukuma daga wannan watan an fara saka musu kudadensu a asusunsu kai tsaye. Duk karamar hukumar da ka daukii ma’aikata dari biyar masu NCE ka gama gigita wannan karamar hukumar.Ka ma dauka za ka dinga ba su naira dubu goma sha biyar-biyar kudin abin hawa daga muhallinsu zuwa inda za su koyar din dari biyar din nan sau dubu goma sha biyar bai wuce miliyan bakwai da dubu dari biyar ba amma serbice din da cire mutane daga cikin kangi ba karamin ci gaba ne. Su sun san ba aiki suke ba amma ka ba su abin yi ka rage masu zaman banza ka samar musu da lasisin samun bashi. Muna nan muna ta wannan tunanin. Wannan wasu kadan daga cikin ire-iren shawarwarin da muke so mu ba wa gwamna kenan.

 

Mene ne ka ke gani ya zama mataki na nasararka?

Hakuri. Wato ba don mun yi hakuri ba da wannan hirar da muke yi da ke da ma ba ki zo kin yi ba saboda da tuni an babbata da ni da tuni na debe kayana a siyasa saboda tun daga farin tafiyar zuwa yau an samu abubuwa na bacin rai da dama a tafiyar siyasa amma mun yi hakuri shi yasa muka kai har zuwa yau. Hakurin nan ya sa na rike dukkan mukaman nan. Sau biyu fa ina rike shugaban jam’iyyar PDP rashin hakuri ai ba zai ba ka wannan ba. Ai ban fi kowa kwarewa ba amma sai aka hada kwarewar da hakuri Shi yasa yanzu ma kana zaune za ka ga an zo an neme ka. Sai ma nan gaba tunda kullum ana kara samun kwarewa ne. Sannan irin gwagwarmayar aiki tun daga malamin makarantar firamare har zuwa aiki da muka yi zama da Farfesoshi ‘yan Kudu wanda su suke ganinma kamar in ka fito daga arewa ba ka ma iya Turanci ba ni kuma abin da na koya a NCE dina Turanci ne da Tarihi don haka mutum dai in dai ba Tuturatu ce ta haife shi ba uwar Turawa kasan ba zai tsere min a Turanci ba.

 

A siyasa yadda ka gada, kai ma ka samu magaji ko tukunna dai?

Ita siyasa Ra’ayi ce ba ka cewa lallai sai wane ya gaji wane amma dole a sami me ra’ayinta sannan kowanne yaro da irin dabi’arsa da halayyarsa. Ni duk da gidanmu siyasar ake yi to ban hana ‘ya’yana yi ba amma fa kowa yake son siysa cikinsu sai ya je ya zama yana da kyakkyawar mu’amala da mutane sai ka ki abin ka saboda da mutane, sannan in lokaci ya yi su ba ka dama. su za su mara musu baya kamar yadda nima lokacin da na fito na fara siyasar mutane daga GNPP da PRP da NRC da SDP ga shi nan Hatsin bara su suka ba ni kwarin gwiwa suka cicciba ni saboda siyasa a na yin ta ne saboda mutane. Ina maraba da dana in ya ce zai yi harkar siyasa.

 

Mene fatanka a karshe?

Fatana yadda muka fara muka yi iyakar kokarinmu muka kafa tare da yin reno tunda da ni aka kafa wannan dimokaradiyyar mun shiga majalisa mun yi fada da Obasanjo akan ita dai Damokaradiyyar don ta dore. A lokacin da na bar majalisa albashina dubu dari da bakwai ne nawa na kashin kaina dubu tamanin da bakwai dubu hamsin na ma’aikatana masu yi min gadi a Kano da Abujan da me girki da wanki da direba da sauransu. Har 2003 da muka bari kuma Alhamdillah mun kafa dimokaradiyyar don haka kullum muke jin ina ma da dama in ka wuce aka kira ka aka ce kai sanata ne a gaban goshinka a san na wanne shekara ne.

Ba a bin da zan fadawa Allah sai godiya duk wani abu da zan zama a rayuwa kawai Bonus ne kusan duk abin da nake fatan Allah ya yi min a rayuwa ya yi min. In ya kara min ina so in kuma ya bar ni haka, Alhamdlillah.

Exit mobile version