Faeza Mustapha">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Gyara Kayanka Baya Zama Sauke Mu Raba

by Faeza Mustapha
January 19, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Gyara Kayanka Baya Zama Sauke Mu Raba
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitinta na sulhu, sun yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa jami’an shirin wanzar da zaman lafiya na majalisar dake aiki a Mali, ranar Juma’ar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’in shirin dan kasar Masar, tare da jikkatar wani guda.

samndaads

Kamar yadda kullum majalisar Dinkin Duniya ke nanatawa, hari kan jami’an wanzar da zaman lafiya ka iya zama laifin yaki karkashin dokokin kasa da kasa. Abun lura shi ne, jami’an wanzar da zaman lafiya ba su da mummunar manufa, manufar su ita ce gyara da tabbatar da zaman lafiya domin kowa ya rayu cikin kwanciyar hankali. Su ma mutane ne kamar kowa, suna da iyaye da iyalai, amma suka zabi su sadaukar da zama tare da su, domin samar da kwanciyar hankali ga daukacin al’ummar duniya. Sai dai abun takaicin shi ne, maimakon girmama su da mutuntawa da kuma kare su, sai suke zama wadanda suka fi fuskantar bazarana. Burinsu shi ne, su ga jama’a cikin kwanciyar hankali da walwala, domin su ma su koma gida ga nasu iyalan. Sai dai, abun ba haka yake ba a wajen marasa kaunar zaman lafiya, domin daukarsu suke a matsayin abokan gaba, idan suke mayar da akalar fadansu zuwa kan wadanda ke da kyakkyawar manufa.
An kafa shirin MINUSMA ne a shekarar 2013, bayan kungiyoyin ’yan ta’adda sun kwace iko da manyan garuruwan dake arewacin kasar Mali a shekarar 2012. Kuma tun bayan kafuwarsa, an yi ammana cewa, yanayin tsaro a kasar yana ingantuwa, saboda kokarin da shirin ke yi. Amma abun takaici shi ne, jami’an MINUSMA da fararen hula a kasar, na ci gaba da zama mafiya fuskantar barazana. A cewar majalisar Dinkin Duniya ma, shirin wanzar da zaman lafiya na MINUSMA, shi ne ke cikin hadari mafi muni, cikin dukkan shirye-shiryenta na wanzar da zaman lafiya a duniya. Zuwa watan Disamban 2020, jami’an shirin da suka hada da fararen hula da sojoji 231 ne suka rasa rayukansu, kuma daga cikinsu, 134 sun mutu ne sanadiyyar munanan hare-haren da ake kai musu. Baya ga wadancan, wasu jami’ai 358 sun ji mummunan rauni.
Akwai bukatar bangarori masu rikici da su fahimci manufar shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya da jami’an dake sadaukar da rayukansu wajen ganin sun rayu cikin kwanciyar hankali. Kuma gyara suke yi ba wai danniya ko mulkin mallaka ba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Ziyarci Cibiyar Wasan Dusar Kankara Ta Kasa

Next Post

Gobara Ta Kona Kasuwar Sakkwato

RelatedPosts

A Shirye Sin Take Ta Karfafa Musayar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Amurka

A Shirye Sin Take Ta Karfafa Musayar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Amurka

by Faeza Mustapha
4 hours ago
0

Daga CRI Hausa Ministan cinikayya na kasar Sin, Wang Wentao...

Bukatar Ma je Hajji Sallah

Bukatar Ma je Hajji Sallah

by Faeza Mustapha
4 hours ago
0

Daga CRI Hausa Da alamun har yanzu wasu kasashen yamma,...

Sin Tana Adawa Da Yadda Birtaniya Ta Yi Amfani Da Dandalin UNHRC Domin Shafa Mata Bakin Fenti

Sin Tana Adawa Da Yadda Birtaniya Ta Yi Amfani Da Dandalin UNHRC Domin Shafa Mata Bakin Fenti

by Faeza Mustapha
4 hours ago
0

Daga CRI Hausa Yau Laraba yayin taron ganawa da manema...

Next Post
Gobara Ta Kona Kasuwar Sakkwato

Gobara Ta Kona Kasuwar Sakkwato

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version