Gyara Kayanka: Illolin Shaye-Shaye Mara Misaltuwa

Da farko dai ita harkar ta’ammuli da miyagun kwayoyi da sauran ire-iren kayan maye abu ne wanda ya daDe yana ci ma al’umma tuwo akwarya musamman a irin wannan lokaci da muke ciki.

Harkar shaye-shaye abu ne wanda ke kawoma al’umma koma-baya mai makon cigaba. Yana daga cikin illar shaye shaye  karuwar yawaitar mahaukata musamman matasa wanda su ne kashin bayan ko wace al’umma a duniya. Shaye-shaye yana haifar da cututtuka da yawa a jikin Dan Adam musamman abin da ya shafi kwalkwalwa da zuciya da dai sauransu.

Yana daga cikin illar shaye-shaye mutum ya dinga Debe tsammani da samun rayuwa ingantacciya irin ta sauran mutane domin kuwa idan har mutum ya kai wani lokaci yana cigaba da shaye-shaye tabbas za ka same shi yana tsince-tsincen kayan bola daga nan kuma shikenan ya kama hanyar tafiya kenan.

Babban abin takaice da ban kunya bai tsaya a kan matasa ba kaDai yanzu har ma da matan Aure da manyan mazaje sun kama harkar shaye-shaye haikan wanda su ya kamata a ce suna wa yara faDa a kan irin wannan halin. Akwai ‘yan mata da yawa waDanda na sani sakamakon biye ma kawaye da samarin banza ya kaisu ga faDawa cikin harkar tsundum! Wannan abin tausayi ne matuka domin idan ba Allah ya ceto su ba, haka rayuwansu za ta kare a banza, maganan aure kuwa shikenan sun yi hannun riga da ita.

Akwai alamu wanda yakamata  iyaye su rika lura da su game da yaransu ta inda za su iya ganewa idan har Dansu ko ‘yarsu ta fara shaye-shaye, sun haDa da: yawan barci babu kakkautawa kowani lokaci ko kuma yawan kife kai daga cikin jama’a ko kuma a wani lokuta za ka ga mutum ya yi shiru ko magana kake masa ba zai amsa maka ba, a wani lokaci kuma za ka ji mutum shikaDai yana surutu wani zibin ma har da dariya. WaDannan kaDan ne daga cikin alamomi wanda ya kamata iyaye su rika lura da su akan sha’anin yaransu.

Akwai daga cikin yara ba a cika saurin gane su ba idan sun fara shaye-shaye sai an bi wasu hanyoyi da dama, amma cikin irin hikima da Ubangiji ke saka wa iyaye wasu sai ka ga sun gano halin da yaransu ke ciki. Gaskiyar magana shaye-shaye na kawo mana abubuwa marasa kyau da yawa a cikin kasarmu kamar su rashin tausayi, rashin imani, sace-sace, fashi da makami, karuwanci, rashin ganin mutuncin manya da dai sauransu.

Ina kira ga ‘yan siyasa da su ji tsoron Allah s udaina amfani da matasa wurin cimma burinsu na siyasa ta hanyar siya masu kayan maye domin su yi masu bangan siyasa. Ku ‘yan siyasa ku tuna fa kuma kun haifa, me zai hana ku yi amfani da ‘ya’yanku wurin siya masu kwayoyi domin su yi maku bangar siyasa ba? Sai ‘ya’yan talakawa da basu san ‘yancinsu ba, a kan naira dubu Daya a haDa mu faDa da ‘yan uwansu, don Allah ‘yan siyasa ku dunga taimaka ma matasa da aikin yi ne ba siya masu kayan maye ba.

Daga karshe kuma, ina kira ga al’ummar Nijeriya baki daya kada mu rika kaurac e masu, ma’ana  su ‘yan uwanmu da suke cikin wannan hali kamata ya yi mu dinga jawo su a jiki domin basu shawarwari da kuma nuna masu irin illar da ke tattare da ita, saboda idan muka ce mun kaurace masu kwata-kwata mu tuna fa wasu waDanda babu ruwansu za su janyo su su shiga tasu harkar, a nan an samu cigaba ne ko cibaya? Allah ya ba mu ikon fin karfin zukatunmu waDanda suke cikin irin wannan hali kuma muna rokon Allah ka shirya mana su. Allah ka kara wa kasarmu zaman lafiya da karuwar arzikin amin.

Daga Bashir Saleh  U/Rimi Kaduna.

08061147018

Exit mobile version