Gyara Kayanka… ‘Mijina Bai Taba Faranta Min Rai Ba!’

Daga Bello Hamza

An tambayi wata mata ko mijin ta na faranta mata rai—amsarta zai ba ka mamaki.

Wannan abin da ya kamata duk mace karanta ta karanta ne kuma ta fahimta in har tana son samar da iyali ingantacce.

A lokacin wani darasi a Jami’ar Pacific, malamin ya tambayi wata mata cikin masu saurarensa, shin mijin ki na faranta maki rai?

A dai dai wanan lokaci sai mijin ya gyara tsayuwa yana tsammanin matar za ta ce ya na faranta mata rai domin tun da su ke ba ta taba yi masa korafin wata matsala ba.

Amma, sai matar ta kada baki ta a’a “miji na ba ya faranta mani rai”

Mijin ya rude, ita kuma ta ci gaba cewa, “miji na bai taba faranta mani rai ba kuma ba zai taba faranta mani rai amma hakika ina cikin farin ciki”

“farin ciki da bakin cika bai dogara ga miji na ba, farin ciki nay a doru ne a kan kai na” in ji ta

Ta kuma kara da cewa, “na kuduri kasancewa cikin farin ciki ne a kowanne hali a rayuwa na saboda in har na dora farin ciki na a kan wani ko wani abu a duniyan nan to lallai zan shiga rikici”

Dukkan wani abu a bayan kasa na canzawa, tun da ga dan adam shi kan sa da dukiya da jiki na da abokai da jin dadi da duk yanayin da ki ka samu kan kina lafiya da rashin lafiya. Na jadda da kasancewa cikin farin ciki a kowanne hali, ko ina shi ko babu, ko ina cikin gida ko waje.

Ina da miji amma tun kafin in yi aure na ke cikin farin ciki, ina farin ciki da kasancewar kai na.

 

Akwai wasu mutane da kan shi ga tsananin bakin ciki saboda rashin lafiya ko rashin kudi ko saboda sanyi ko zafi ko wani ya zage su ko wani ya daina son su mijin ta ya canza ko ‘ya’yansu su sun canza ko abokanansu sun canza mu su ko kuma sun samu matsala a wajen.

Ni dai ina son rayuwa, ba wai domin ban i da wata matsala ba amma domin na kudurci kasancewa cikin farin ciki, farin ciki na a hannu nay a ke.

In na dauki wajibcin kasancewa da wani to na kan sauke mu su dawainiyar hakkin farin ciki na , hakan na sa rayuwa ta yi sauki. Hakan ne kuma sirrin zama na a gida miji na tsawon wadannan shekarun.

Kada ka bai wa wani daman sarrafa farin cikin ka, kasance ckin farin ciki ko a na zafi ko ba ki da lafiya ko ba ki da kudi ko wani ya cutar da ke ko kuma wani ya dai na son ki ko kin dai na ganin mahimmaacin kan ki.

Wannan abin lura ne ga mata da maza ko mi tsufansu.

Exit mobile version