Abdulyassar Aminu Abubakar" />

GYARA KAYANKA: Wasikar Malam Aku (5)

Tare Da: Abdulyassar Aminu Abubakar, 08093824782  abdulyassaraminu782@gmail.com

A yaruka na duniya tabbas yaren Hausa na daya daga cikin yarukan da a ke ji da su a fadin duniyar nan, tun daga yanayin mu’amala, kasuwanci, tarayya da sauransu. Amma a wannan kazamin lokacin da mu ka shigo babuy wani yare da yake sakin al’adar shi ya dauki ta wani yaren sama da yaren Hausa.

Na taba tambayar wani Malami dangane da wasu daga cikin al’adun Hausawa, sai ya bani amsa da cewa, “Al’adun Malam Bahaushe akasarinsu ba su yi wa addinin musulunci shisshigi ba, ma’ana bas u sabawa addinin ba, amma ina nufin a baya kafin abin ya lalace kamar yanzu.”

Kwarai Malam ya yi gaskiya da ya ce a baya, shin wai iyaye ba su lura ne da irin dabi’ar da diyansu suke dora ta ga kawunansu ba? Ko kuwa suma za su yi amfani ne da yanayin yadda zamanin yake tafiya su ce ai burgewa ce?

Yayin da aka tashi yin bukin aure za ka ga saurayi da budurwar sai hotuna suke yi suna rike da juna ko kuma su kara jukkunan su iyaye kuma suna gani sun kyale alhalin kuma muharraman juna ba su zamo ba.

Suturar Bahaushe  a bangaren mata, shi ne a sanya riga, zane da hijabi a rufe dukkan jiki haka ma addininmu ya zo da shi ko da kuwa ta bangaren maza ne ma sai dai amma a wannan zamani na mu irin waccan shigar ma kauyanci ce da rashin waye wa. Wajen buki na je sai na ana wani abu da ake cewa da shi (IGBO DAY), yanmata ne suka sanya sutura sak ta Inyamurai babu hijabi babu mayafi saiu kayan da aka sanya su ma kuma irin dai na Inyamurai ka rantse da Allah ba diyan Hausawa ba ne, haka su ma mazan na ga sun yi irin waccan shiga inda suka sanya zane da singileti da wata jar da dara, suka sanya murjanai a wuya kai ka ce mata ne su ma. Haka manyan mata suka sanya su gaba da ‘yan gari ana kallon su suna ta rawa ana sowa kuma abin haushin ba irin wakokinmu ba ne na Hausa ba.

Idan har batun kayan lida ake yi ai ba a kai ka ba, kai ke da ganga, jinjima, kukuma, kuntugi ga kuma goge da kwarya ta kidan mata duk wannan ba su ishe ka ba sai ka yi aron na wasu? Aladunmu tuni an rigada an baro su a baya ba kuma za a taba dawo da martabar su ba, ba zan mance da wani baiti daga cikin wakar Alhaji Akilu Aliyu ta HAUSA MAI BAB HAUSHI BA inda yake cewa, “ Tafiya fa ta yi tafiya mu lura mu juyo. An kada mu mu yi kokarin shan fansa. Abu na mu ne mu rike shi kankam ya fi. In mun yi wasa dole zai mana nisa. Mu rike kaho ke nan a more mu tatsa. Nono a sha mu sai suda mi lasa. An barmu gangambu kago ba jinka. Wasu can su sha inuwa bagas lallausa. To kun ga aiki na mu ci na wadansu. An karkasa musu arha sai su yi kwasa. Ba cas bare as ba da kauda kara ba. Suwadadas suke su sha bungasa.”

Idan mutum Bahaushe ne dole zai fahimci babu komai a cikin wakar nan illa karin maganar da ake yi kan ka da Bahaushe ya saki al’adarsa ya riki ta wani amma kuwa baitin wannan waka ba a yanzu zai yi tasiri ba sai a sanda mu ka waiwaya mu ka nemo al’adunmu mu ka rasa su a sannan ne kuma za a rika cizon yatsa ana dan dama. Gyara kayanka dai ba ya taba zama sauke mu raba, haka zalika shi fa gyara ya fi batawa.

Exit mobile version