Tsohon daratan sashin kasafin kudade a Babban Bankin Nijeriya (CBN), Dakta Titus Okunrounmu ya bukaci gwamnatin tarayya da mayar da hankali wajen kokarin gyara matatun kasar nan, domin gyara matatun kasar nan ne kadai hanyar farfado da tattalin arziki a shekarar 2021. Okunrounmu ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Ota da ke cikin Jihar Ogun.
Ya ce, “akwai bukatar kasar nan ta sake gina matatun mai tare da gyara matatun man da ake da su, idan ana son farfado da tattalin arziki a shekarar 2021,” in ji shi.
Ya kara da cewa, babu wata kasa da take sayar da danyan mai a kasuwan duniya kuma ta zuwa tana siyo man da aka tace a kasashen ketare sai dai kasar Nijeriya. Ya ce, ya kamata kasar nan ta daina shigo da mai ta yi kokarin gyara matatun mai wanda zai sa a dunga zuwa Nijeriya ana sayan tataccen mai. Tsohon daraktan ya ce, bayar haka kuma, yana da matukar mahimmanci a wadata ‘yan kasa da tataccen man fetur ta yadda za a samu nasarar samun karin kudaden shiga masu yawan gaske. Ya kara jaddada cewa, idan ana tace man a Nijeriya, za a samu damar fitar da wasu man zuwa kasashen ketare kamar irin su man jirgi da man inji da dai sauran su, sannan kuma har ila yau za a ci gaba da fitar da man fetur din a sauran kasashe da ke fidin duniya, wanda zai kara sa Nijeriya ta ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci da sauran kasashe tare da samun kudaden shiga masu yawa marasa adadi. Ya ce, matukar gwamnatin tarayya ba ta dauki matakin daina shigowa da mai kasar nan ba, to zai yi wahala a sami wani canji a bangaren tattalin arziki a shekarar 2021.