Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home MANYAN LABARAI

Gyaran Iyakokin Mazabu: Ina INEC Ta Sa Gaba?

by Muhammad
March 9, 2021
in MANYAN LABARAI
5 min read
Mazabu
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Nasir S. Gwangwazo,

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Cin Gashin Kan ta (INEC) ta bayyana irin aikin da ya rataya a wuyan ta wajen aikin gyaran iyakokin mazabun dake kasar.

Babban Kwamishinan Kwamitin Yada Labarai da Wayar da kan Jama’a na hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Okoye ya ce hukumar ta lura da wasu rahotanni da ke yawo a kafafen yada labarai daban-daban a kan hakkokin hukumar wajen rarrabawa, sake nazari da kuma gyara kan iyakokin mazabu a Nijeriya.

Ya ce ganin haka ne ya sa tilas hukumar ta ga ya kamata ta fito ta bayyana matsayin ta a bisa tsarin mulki a wannan aikin.

Ya ce, “Saboda a tabbatar da fahimtar jama’a kan al’amarin, hukumar na so ta yi bayanin abin da tsarin mulki ya dora mata da kuma abin da ta ke yi a kan hakan.

“Da yake karkasa kasar nan zuwa zuwa mazabun Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da Majalisun Jihohi hakkin hukumar ne, da zaran an fitar da su, sauran aikin sake nazarin mazabun tare da ko yi masu kwaskwarima aikin hadaka ne na ita hukumar da Majalisar Tarayya.

“Saboda haka, duk wani sake tsari ko gyara irin wannan ba zai yiwu ba sai bangarorin nan biyu na Majalisar Tarayya sun amince da shi, wato Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai.”

Okoye ya bayyana cewa a dalilin wannan muhawarar, hukumar ta na zantawa da  kwamitocin Majalisar Tarayya da su ka dace  domin a shirya zama da shugabannin majalisar saboda a tunkari wasu daga cikin manyan matsalolin rarrabawa da sake nazari da kuma gyaran mazabun a Nijeriya.

A cewar sa, wasu daga cikin matsalolin, wadanda a baya hukumar ta nuna wa Majalisar Tarayya su, sun hada da wadannan:

“Tsarin Mulki na 1999 (a yadda aka yi masa kwaskwarima) bai dora wa INEC alhakin sake nazari ko sauya kan iyakokin mazabu ba bayan kowane shekara 10, kamar yadda aka fada a wasu ra’ayoyi a kafafen yada labarai. Don cire duk wani shakku, Sashe na 73 (1) na Tsarin Mulki ya tanadi cewa aikin zai rika faruwa jefi-jefi ‘mafi karancin shekara 10’.”

“Hakan ya nuna cewa za a iya yin hakan ne kadai daga shekara 10 zuwa sama. Don haka, hukumar ba ta saba wa Tsarin Mulki ba, tunda dai za a iya sake nazarin ne a cikin shekara 10 kadai zuwa sama.

“Haka kuma Tsarin Mulki ya tanadi cewar hukumar za ta iya fara aikin sake nazarin da yin gyaran idan an gudanar da aikin kidayar jama’a ta kasa, kirkiro jihohi ko idan Majalisar Tarayya ta zartar da Doka [Sashe na 73 (2)]. A yanzu babu ko daya daga cikin wadannan abubuwan da su ka faru.

“Aikin kidayar jama’a na karshe da aka yi an yi shi ne a cikin 2006, kimanin shekara goma sha biyar kenan.

“Hukumar ta na ganin cewa sake nazari ko tare da sake tsarin mazabun bisa  bayanan shekara 15 da aka tattara bai dace ba saboda kowa ya san saurin karin yawan jama’a da ake samu a Nijeriya zai sa a ga shirme a duk wani sakamako da aka samu.

“Ko ma dai yaya ne, Hukumar Kidayar Jama’a ta Kasa ta na nan ta na kokarin sake wani aikin kidayar kuma akwai alamar dacewar a jira a ga sakamakon shi.

“Ta wani bangaren, ba a kirkiro wasu sababbin jihohi ba a Nijeriya tun daga lokacin da aka yi Tsarin Mulki a cikin 1999 sannan babu wata Dokar Majalisar Tarayya da aka yi mai bukatar d INEC ta fara aiki da wasu sassan Tsarin Mulki da su ka dace da batun karkasawa, sake nazari ko sake tsarin mazabun zabe.”

Kwamishinan hukumar zaben ya kara da cewa a kan batun mazabun jihohi da za a kirkira a kowace jiha ta tarayyar kasar nan, Tsarin Mulki ya tanadi cewa yawan wadanda za a yi a kowace jiha ya kasance ninki sau uku ko sau hudun yawan mazabun tarayya (kujerun Majalisar Wakilai), ya danganta da mafi karancin 24 da kuma mafi yawan 40.

A cewar sa, matsalar ita ce wasu jihohin a yanzu su na da yawan kujerun su har sau uku a Majalisar Wakilai, wasu sau hudu; wasu kuma su na da mafi karancin  24 yayin da wasu har sun kai kurewar 40.

“Wasu, yawan mazabun su na Majalisar Jiha bai kai sau uku ko hudu na yawan kujerun su na Majalisar Wakilai ba.

“Wannan kwamacalar gudunmawar na bukatar a yi cikakken karin bayani kan karkasawa, sake nazari da yin kwaskwarima ga iyakokin mazabun, wanda a gaskiya ya na bukatar gyaran tsarin mulki.”

Okoye ya yi nuni da cewa akwai kuma batun mazabun da ake cewa an danne wadanda mazabu ne da ake da su a da tun kafin a samar da Tsarin Mulki na 1999.

A cewar sa, mutanen da ke kamfen din a kirkiro masu da wadannan mazabun su na cewa an “danne” su ne a halin da ake ciki ba.

Ya ce, “An shigar da kararraki arba’in da biyu a kotuna daban-daban a sassan kasar nan inda ake bukatar a tilasta INEC ta ‘dawo’ da mazabu sittin da biyu.

“Hukumar ta na ta bayyana cewa batun ‘dawo da mazabu’ akwai ayar tambaya a kan sa a shari’ance sannan kuma akwai ayar tambaya wajen yiwuwar sa a zahirance.

“Akwai ayar tambaya a ce wai INEC ta dawo da mazabu wadanda aka yi a karkashin wani tsohon tsarin mulki zuwa cikin na yanzu. Misali, Tsarin Mulkin yanzu ya tanadi cewa kujerun Majalisar Wakilai kada su haura wani yawa kuma ninki su ne a mazabun Malisar Jiha. Dawo da dukkan tsofaffin mazabu daga tsoffin tsarin mulki ba shakka zai nuna cewar yawan kujerun da Tsarin Mulkin yanzu ya tanadar zai karu.

“Bayan haka ma, akwai tsare-tsaren mulki daban-daban da aka yi a baya, kowanne da nasa iyakancewar yawan mazabun.

“Bugu da kari, wanne ne daga cikin tanadin abin da tsarin mulki za mu dawo da shi? Watakila wasu mutanen za su ma nemi a dawo da mazabu hudun da ke Kalaba da Legas wadanda aka kirkira a cikin 1922 bayan an kirkiro Tsarin Mulkin Clifford Constitution.

“Haka kuma ba daidai ba ne a yi maganar mazabun da aka danne saboda wasu daga cikin mazabun an raba kasar su a dalilin kirkiro jihohi tare da gyaran kan iyaka, da kirkiro Yankunan Kananan Hukumomi, da kuma kirkiro  mazabun zabe da ake da su yanzu.

“Wasu daga cikin hukunce-hukunce da kotuna su ka yanke kan batun nan na mazabun da aka danne  sun amince da matsayar hukumar, yayin da wasu sun koma ga masu kamfen din ‘mazabun da aka danne’. Sannan a wasu shari’un, hukumar ta daukaka kara.

“Wadannan su na daga cikin matsalolin da su ka takura hukumar a kan batun sake nazari da gyaran kan iyakokin mazabu. Duk da haka, ba wai hukuma ba ta sane da muhimmancin daidaita fitar da iyakokin mazabu ba a tsarin mulkin dimokiradiyya da tsarin gudanar da zabe ba.

“Amma dai wadannan wasu al’amura ne masu sarkakiya a shari’ance da siyasance da kuma zahirance. Hakan ne ya sa hukumar ta bukaci ta zauna tare da shugabannin Majalisar Tarayya domin a warware wadannan al’amuran, tare da samar da matsayar da ake bukata wadda za ta tabbatar da cewa duk wani sake nazari da za a yi na mazabu zai samu amincewar Majalisar Tarayya, ba kamar yadda ake yi a baya ba inda majalisar ba ta amince ta bukatun hukumar ba kan sake nazari da yin sauyi a mazabun.

Okoye ya ce, hukumar a yanzu haka ta na nan ta na tsara cikakken kundin tattaunawa kan wadannan al’amura wanda zai taimaka wajen taron da za ta yi da Majalisar Tarayya.

Ya ce, “Hukumar ta na so ta bayyana wa duniya duk wata tattaunawa ta fahimtar juna da shugabannin kwamitoci daban-daban na Majalisar Tarayya da neman goyon bayan jama’a don tabbatar da an samu kyakkyawan yanayi da zai ba hukumar damar ci gaba da yin aikin ta a kan hakan.

“Don nanatawa, haka kuma hukumar na so ta bayyana cewa batun mazabun wani abu ne daban kuma bai da alaka da aikin tuntubar da ake yi yanzu kan samar da karin yawan rumfunan zabe a Nijeriya.”

SendShareTweetShare
Previous Post

CP Alabi Ya Zama Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi

Next Post

‘Yan Banga A Neja Sun Shirya Yaki Da ‘Yan Ta’adda

RelatedPosts

Dattawa

Fafutukar Ma’aikatan Shari’a Ta Samu Tagomashin Majalisar Dattawa

by Muhammad
53 mins ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, A ranara Litinin fafutukar da ma’aikatan...

Soji

Karuwar Hare-hare: Ministan Tsaro Da Manyan Hafsoshin Soji Sun Yi Dirar Mikiya A Maiduguri 

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Muhammad Maitela, A ci gaba da daukar ingantattun matakan...

NULGE

Yadda NULGE Neman Mamaye Gidajen ‘Yan Majalisar Dake Goyon Bayan Kudirin Cire Kananan Hukumomi

by Muhammad
2 days ago
0

Dga Rabiu Ali Indabawa, Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Nijeriya...

Next Post
‘Yan Banga A Neja Sun Shirya Yaki Da ‘Yan Ta’adda

'Yan Banga A Neja Sun Shirya Yaki Da 'Yan Ta'adda

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version